Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewar yana da yakinin cewar ko yanzu idan ya bukaci ‘yan Nijeriya su tara masa kudi domin ya wake shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi imani za su tara masa.
Yayin fira da jaridar Trust Nig Hausa ya bayyana cewar ‘yan Najeriya na matukar kaunar shugaba Bola Ahmed Tinubu don haka baya tsammanin su kasa hada masa kudin wake Tinubu idan ya bukaci hakan.
Ina mai tabbatar maku cewar duba da yadda al’ummar kasarnan ke matukar kaunar Tinubu idan na bukaci su tara mani kudi domin wake shi za su tara.
Rarara dai ya taba neman ‘yan Nijeriya su tara masa kudi domin ya wake tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021 wanda kuma a wancan lokacin Rarara ya yi ikirarin cewar ya samu makudan kudade ta sanadiyar tura masa kudi da masoyan tsohon shugaban kasar suka yi.
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Babban abokina Haruna Talle Mai Fata.
Da wanne jarumi ko jaruma ka fi son yin fim da shi?
Ali Nuhu da Adam A Zango, mata kuma ba ni da zabi gaskiya.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Na kawo ci gaban da ba a taba tunani ba da izinin Allah.
Ya alakarka take da sauran abokan sana’arka?
Muna zaune lafiya, muna ganin darajar juna.
Wanne irin kalubale ka fi fuskanta wajen gudanar da ayyukanka, kuma ta wacce hanya ka ke ganin za a shawo kan matsalar?
Kalubalen da na samu shi ne; Dana rike iya fim shi ne sana’ata, saboda duk wanda ya rike iya fim shi ne sana’arshi ba shi da sana’a, dole ka zama dan kasuwa. Duk sana’ar da ba za ta kawo maka 500 ko 1000 kullin ba, ba sana’a ba ce. Ya kamata duk wani dan fim ya zama yana da ‘plan’, ko wajan cajin waya ne ka tsira da shi, shi ne gaskiyar magana, dan har kana so ka zauna da iyalanka lafiya da kuma iyayenka da abokanka da ‘yan uwa ba za ka dame su da roko ba.
Za mu ci gaba.
Source LEADERSHIPHAUSA