Wani matashi mai amfani da TikTok ya wallkafa dan gajeren bidiyo da ke nuna lokacin da ya gwangwaje mahaifiyarsa da kyautar zagayowar ranar haihuwa na musamman.
Bidiyon ya hasko yadda wannan matashi ya kullewa mahaifiyarsa fuska sannan ya tuka ta zuwa filin jirgin sama, inda ya cika ta da mamaki.
Yanayin mahaifiyar bayan ta amshi kyautar ba zatan ya tsuma zukata, yayin da mutane da dama suka taya su murna.
Wata uwa ta samu abun da ta dade tana mafarkin samu a ranar zagayowar ranar haihuwarta lokacin da danta ya shirya mata wata tafiya ta bazata.
Bidiyon da ke nuna lokacin jin dadin na tsakanin uwa da danta ya yadu a dandalin TikTok.
“Ya Sa Ni Kuka”: Matashi Ya Gwangwaje Mahaifiyarsa Da Kyautar Zagayowar Ranar Haihuwa Na MusammanHoto: @kelly_khobbi Asali: TikTok A bidiyon wanda @kelly_khobbi- blue ya wallafa, an gano uwar zaune a cikin wata mota yayin danta da sauran mutane da ke motar suka rufe mata fuska.
Bayan sun isa inda za su, wanda ya kasance filin jirgin sama, sai aka jiyo dan nata yana umurtan mahaifiyarsa da ta bude idanunta. Tana aikata hakan, sai ta ga cewa sun isa filin jirgin sama.
Dan nata ya kuma sanar da mahaifiyar tasa cewa sun isa wajen domin tafiya wani waje na daban kuma a cikin jirgi za su yi shawagin da ta dade tana mafarkin yi.
Daga kallon bidiyon mutum zai gane cewa mahaifiyar ta dade tana burin hawa jirgin sama wanda shine kyautar bazata da ta samu daga danta don murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Mahaifiyar ta cike da farin ciki sannan ta dungi murmushin jin dadi yayin da take kallon dan nata.
Ta so ace wando ta sanya wanda take ganin shine zai fi dacewa da yawo a jirgin sama.