Wani magidanci ya bayyana yadda wata ƴar ajin su da ta tsane shi ta zama matar sa ta aure.
Ya bayyana cewa a lokacin suna ajin ƙaramar sakandire, ta tsane shi sosai saboda gajartar sa da yawan rigimar sa.
Ya tuno yadda a baya lokacin tana rubuta masu surutu ta rubuta da shi duk kuwa sa cewa a ranar bai zo makaranta ba.
Wani magidanci ɗan Najeriya, @Hon_Danjo, ya sosa zukatan mutane da dama da labarin soyayyar sa, lokacin da yake mayar da martani kan wata tambaya da aka yi wa ma’aurata sun bayyana yadda suka haɗu da masoyan su.
Hon_Danjo wanda auren sa zai cika shekara biyar a watan Oktoban 2023, ya ce da shi matarsa ajin su ɗaya a JSS1 sannan itace shugabar ajin.
Wannan magidanci ya bayyana cewa kwata-kwata bai yi mata ba domin akwai lokacin da ta taɓa yi masa izgili saboda ya zo da irin abincin eko da alala makaranta a matsayin abincin rana.
Hon_Danjo ya kuma ƙara da cewa ta tsane shi saboda gajartarsa sannan ya cika jan rigima.
Tsanar da ta ke masa ta yi yawan da har ta kai ta rubuta sunan sa cikin masu surutu a aji a wata rana da bai je makaranta ba.
Shekaru bayan wannan abin da ta yi masa ya sanya an bulale shi, yanzu sun zama ma’aurata har sun haifi yara biyu.
A kalamansa: “Itace shugabar ajin mu lokacin muna JSS1.
Ta taɓa min izgili saboda na je da Eko da Alala matsayin abincin rana a makaranta. Ta tsane ni saboda gajere ne ni da rigima ta.”
“Watarana ban je makaranta ba an kore ni gida saboda kuɗin makaranta.
Malamin mu ya ce ta rubuta sunayen ƴan surutu.
Ta rubuta suna na sau 100.”
“Malamin bai bari na yi masa bayanin cewa ban zo makaranta ba ranar ta yaya zan kasance cikin ƴan surutu.
Sun zane ni kamar ɓarawo. Bayan shekaru na haɗu da ita, daga nan soyayyar mu ta fara.
Tun daga nan na cigaba da ɗaukar fansa, ƴaƴan mu biyu su zan nuna a matsayin shaida.”