Batun yawan kudin da ake biyan ‘yan fim a masana’antar shirya fina-finan ta arewacin Najeriya ga alama ya raba kan ‘yan Kannywood biyu.
Tun bayan da BBC Hausa ta wallafa bidiyon hirarta da Hajiya Ladin Cima a filin Daga Bakin Mai Ita, sai ce-ce-ku-ce ya barke kan batun nawa ake biyan jarumai.
Ainihin hirar an yi ta ne ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamban 2021, a lokacin da BBC ta aika ma’aikatanta biyu Kano don tattaro shirin Daga Bakin Mai Ita da wasu ‘yan Kannywood 11. Amma da yake ana saka shirin daya bayan daya ne a kowace Alhamis, shi ya sa na Ladin Cima bai fito ba sai bayan wata biyu da yin hirar.
Hajiya Ladi da aka fi sani da Tambaya ta Malam Mamman ko Mama Tambaya kamar yadda abokan aikinta ke kiranta, ta shaida wa BBC ne cewa ana biyanta kudin da ba su haura naira dubu biyar ba.
Wannan magana ce ta ja hankalin masu bin shafukan BBC Hausa na intanet inda suka dinga zargin furodusoshi da daraktoci da rashin tausayin tsofaffin ‘yan fim din.
Lamarin da ya sosa ran wasu furodusoshin irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi, har suka shaida wa BBC cewa ko su sun taba ba ta kudade masu yawa na fita a fim dinsu da ta yi.
Inda kuma Mama Tambaya ta jaddada wa BBCn cewa an yi haka, bayan sake tuntubarta da muka yi.
Duk da dai Ali Nuhu da aka fi kira da Sarkin Kannywood da kansa ya ce ba za a rasa masu biyan 2,000 ko 5,000 ba, amma bai kamata Ladin Cima ta yi wa duka furodusoshi kudin goro ba.
Wannan hira dai ta zama tamkar bude kofa ne ga wasu abubuwa da suka dade suna ci wa wasu ‘yan masana’antar tuwo a kwarya.
Domin tun daga ranar Alhamis, batun dai da ake ta tattaunawa kenan a shafuka daban-daban.
Su ma sauran al’umma ba a bar su a baya ba don sun shiga zancen dumu-dumu tare da bijiro da tambayoyi kan abubuwa da dama da suka shafi Kannywood.
Girma da habaka irin ta masana’antar Kannywood a wannan zamanin, ta wajen nishadantar da al’umma da samar da ayyukan yi da kudaden shiga ga hukumomi, ya sa bai zama abin mamaki ba don wannan batu ya ja hankalin mutane.
Manyan jarumai irin su Nafisa Abdullahi da Nuhu Abdullahi da Hadiza Gabon da Rukayya Dawayya da Tijjani Asase duk sun dan yi gugar zana a shafukansu na sada zumunta.
Wasu kuwa irin su Adam Zango da Rahama Sadau sai suka nuna alamar bakinsu da goro, wato sun dinke shi duk da dai akwai magana.
Wasu na ganin abin da Hajiya Tambaya ta fada gaskiya ne, wasu na ganin ba ta yi daidai ba yayin da wasu kuma ke nuna babu ruwansu kawai dai suna kallon abin da ke faruwa.
‘Yan ba ruwana
A ranar Juma’a Rahama a shafinta na Instagram ta wallafa Hmmmmmmmmmm da alamar rufe baki.
Adam Zango kuwa a ranar Asabar sai ya wallafa wani bidiyo da ‘yan amshi a bayansa yana wata waka mai taken “Shiru”, inda yake cewa “duk abin da babu ruwanka ka koma gefe ka yi shiru.”
Nafisa Abdullahi a nata sakon kira ta yi ga ‘yan fim cewa su daina karbar aiki idan har farashin da furoduso ya yanka musu bai musu ba.
Duk da cewa ‘yar wasan a shafinta na Tuwita ta bayyana shakku kan batun Ladin Cima, amma ta ce watakila ba abin mamaki ba ne hakan na faruwa.
“Idan ba a biyanka da kyau a aikin da kake yi, kuma kai ka san ka fi karfin hakan, mene ne abin wahala wajen fahimtar da wadanda suka ba ka aikin cewa ka san hakkokinka?
“Mene ne abin wahala ka gaya musu cewa kudin da suke son ba ka bai maka ba?
Magana zarar bunu
Wani bidiyo da Naziru Sarkin Waka ya yi a shafinsa ranar Alhamis za a iya cewa shi ya kara tunzura wasu ‘yan Kannywood din har rabuwar kawunansu ta kara fitowa fili.
A bidiyon ya tabbatar da ikirarin Hajiya Tambaya tare da sukar wasu furodusoshin kan rashin biyan ‘yan wasa.
‘Yan masana’antar irin su Nuhu Abdullahi da Abba Mai Shadda da Alhajin Sheshe da wasu da dama sun yi masa martani a nasu shafukan.
Nuhu Abdullahi ma cewa ya yi “da za mu fito mu yi bayani da mutuncinku ya zube.”
Wasu kuma irin su Ali Artwork sun goyi bayan maganganun Sarkin Waka duk da dai ya yi wasu zarge-zarge kan wasu ‘yan fim din.
Kira ga sulhu
Sai dai duk da wannan tataburza da ake yi, akwai ‘yan Kannywood din da abin bai musu dadi ba ta kowane bangare.
Masu irin wannan ra’ayin na kira ne da a yi sulhu don kar magauta su yi wa masana’antar dariya.
Tijjani Asase da Sahir Abdul na daga cikin masu irin wannan ra’ayi.
Musbahu M Ahmad kuwa wanda yaya ne ga Naziru Sarkin Waka, jan hankalin ‘yan fim ya yi kan su guji furta kalamai marasa dadi da yin gori ga manya daga cikinsu kamar yadda wasu suka rinƙa yi wa Tambaya.
Masu sharhi sun tofa tasuMasu sharhi a lamarin masana’antar irin su Muhsin Ibrahim sun tofa albarkacin bakinsu. A nasa shafin na Facebook ya rubuta cewa ba mamaki karancin kudin da masana’antar ke fama da shi ne ya sa furodusoshi ba sa iya biyan ‘yan wasa da kyau.
“Tabbas Kannywood akwai ƙarancin kuɗi, musamman ga maza da kuma dattijan mata, amma lalacewar bata kai yadda ta faɗa ba. “Ko dan tausayi, na san masu abin hannu a cikin su ba za su ƙyale tsofaffi irin Tambaya ba haka.”