Wata kotu ta shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hoki da ke babban birnin Kano, ta umarci Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh, da ya koma gida ya shirya zuwa wajen bikon matarsa da ta yi yaji.
Wannan Kotu wadda ta bayyana cewar, tunda shi G-Fresh bai saki matarsa ba, akwai bukatar ya yi bikon ta domin cigaba da zaman aurensu.
Lauyar G-Fresh, Barr Fatima Aliyu ta bayyana cewa, har yanzun wanda ta ke karewa na matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba.
Kotun dai ta umurci G-Fresh 25 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba da ya sulhunta da matarsa, Sayyada Sadiya Haruna.
A wani labarin na daban jam’iyyar NNPP ta zargi tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, da hannu kan rashin nasarar da gwamnan Kano, Yusuf Abba, ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar.
Jam’iyyar ta ce Kwankwaso ya sayar da NNPP ga jam’iyya mai mulki ta APC kan tattaunawarsa a batun kujerar minista da ya yi zawarci a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta kori Abba tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a, Oluyemi Akintan-Osadebay, ta janye takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta bai wa Abba Yusuf.
Da ake bayyana dalilan da suka sa aka tsige gwamnan Kano, kotun ta ce ratar kuri’un da jam’iyyar NNPP ta samu ta samu ne ta haramtacciyar hanya ba ta hanyar da ta dace ba, kuma hanyar da ta bi wajen samun kuri’un basu dace da dokar zabe ta 2022 ba.
Alkalan wannan Kotu sun cire kuri’u 165,663 daga jam’iyyar NNPP, inda suka kara da cewa a jikin kuri’un guda 165,663 babu sa hannun jami’in zabe da satamfi da kwanan wata kamar yadda doka ta tanada, don haka suka bayyana cewa kuri’un ba su da inganci.
Da yake mayar da martani, daya daga cikin jagororin jam’iyyar NNPP a yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Abass Akande Onilewura, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis, ya ce rashi da jam’iyyar ta yi a Kano ya tabbatar da zargin kin jinin jam’iyyar da aka yi saboda Kwankwaso.
Onilewura ya jaddada cewa tsohon dan takarar jam’iyyar NNPP na da hannu dumu-dumu da hadin baki da Jam’iyyar APC wanda hakan ya haifar da babban rashi da jam’iyyar ke fuskanta kotunan zabe a Kano.
Ya nanata cewa Kwankwaso bai bi ka’ida ba wajen zabar wasu daga cikin ‘yan takara a jam’iyyar, lamarin da ya ce ya kai shigar da Jam’iyyar cikin halin da ta samu kanta a yanzu.
Source: LEADERSHIPHAUSA