Jarumin masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood), Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da BMB ya ce ya yi danasanin shiga rikicin Ali Nuhu da Adam Zango.
Ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust ta yi da shi, ya bayyana cewa ya dan tsagaita da yin fim amma yanzu haka ya na ta shirya wasu fina-finai.
Ya bayyana cewa ya yi shirme yayin da ya zabi bangare daya a fadan Adam Zango da Ali Nuhu wanda sai daga baya ya gane ba daidai ba ne, amma tuni ya nemi afuwar Ali Nuhu.
Jarumin fina-finan Hausa, wanda furodusa ne kuma darekta, Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da BMB, ya bayyana shirin sa na dawowa sana’ar fim da sauran abubuwa dangane da rayuwarsa, rahoton Daily Trust.
A tattaunawar da Daily Trust ta yi da BMB, ya fara da gabatar da kansa inda ya ce: “Suna na Bello Muhammad Bello, an fi sani da General BMB.
Ni furodusa ne, darekta ne, jarumi sannan mai rubuta labari kuma na tashi ne a cikin rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato.
Kuma na yi makarantar firamaren addinin musulunci daga nan na zarce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Riyom.”
Ya ketare Najeriya don ci gaba da karatu.
Ya ci gaba da bayyana yadda ya ketare Najeriya zuwa kasar Jamus daga nan ya zarce Belguim inda ya so zama gaba daya.
Bayan tunanin shiga harkar Kannywood sai ya dawo don ya bayar da gudunmawarsa don bunkasa masana’antar.
Ya ce bayan dawowar sa harkar fim ne ya koma jami’ar Jos inda ya yi karatun diploma a harkar aikin jarida sannan ya yi wata diploma a fannin kasuwanci kuma a 2005 ya koma fannin tattali ya yi degree daga jami’ar Jos.
An tambaye shi dalilinsa na barin harkar fim inda ya ce bai bari ba.
Yanzu haka ya na ta ayyuka ne akan fina-finansa masu dogon zango wadanda zai saki nan ba da dadewa ba.
Yayin da ake tambayarsa abinda ya fi faranta masa rai a lokacin yana tsundum a harkar fim, inda ya ce gayyatarsu da aka yi zuwa Amurka inda su ka samu karin ilimi.
Ya ce ya yi nadamar shiga fadan Ali Nuhu da Adam Zango Bayan an tambaye shi idan akwai abubuwan da ya yi wadanda yanzu haka ya ke danasani a matsayinsa na jarumi, ya ce akwai, inda ya ci gaba da cewa: “Maganar gaskiya akwai.
Na yi nadamar shiga rikicin Jarumi Ali Nuhu da Adam Zango.
Na yi kuskure da na saurari bangare daya ba tare da na saurari dayan ba.
“Sai daga baya na gane kuskurena akan yadda na yi hukunci na mara wa bangare guda baya.
Na yi danasani duk da dai na nemi yafiyar wanda na yi wa laifin, wato Ali Nuhu.”
Ya Bayyana Dalilin Rashin Yin Auren sa Da Wuri
Ya ci gaba da cewa yana da alaka mai kyau da Ali Nuhu kuma tun bayan ya yafe masa sun ci gaba da alaka.
A batun aure kuwa, ya ce jarumar fim ya aura, Zainab Yunusa, wacce ta haska fim dinsa mai suna ‘Uwar Miji’ kuma shekarun su 5 yanzu haka da aure inda Allah ya albarkace su da tagwaye.
Source: LEGITHAUSA