Kundin tarihi na Guinness ya ayyana cewa, mage mafi dadewa duniya sunanta Flossie kuma daga kasar Burtaniya take.
Flossie ta rayu akalla shekaru 26 da kwanaki 329, wanda daidai kwanakin suke idan kwatanta da shekaru 120 ga dan Adam.
Wannan halitta ta rayu tsawon shekaru duk da kuwa ta zauna a hannun jama’a da dama, daga gida zuwa gida.
Mage mafi dadewa a duniya inji kundin ajiye tarihi na Guinness ‘yar shekaru 27 ne, kuma daga kasar Burtaniya.
Magen mai suna Flossie ta shekara 26 da kwanaki 329 a duniya, wanda yake daidai da shekaru 120 da dan Adam zai yi a duniya, lamarin da ya ja hankalin jama’a.
Kamar dai sauran dabbobi masu jini a jika kuma suke kan ganiyar samartaka, wannanr kyanwa na nan cikin koshin lafiya, amma ba ta gani sosai kuma ta rasa jinta kadan.
Ya rayu a gidaje daban-daban
Flossie, wacce aka ce tana kaunar abinci da kuma kwanciya a jikin mutane, ta rayu rayuwar jin dadi a gidajen mutane da dama.
Mai wannan dabba a yanzu, Vicki, ta bayyana cewa, duk da kyanwar ba ta gani da kyau, tana iya fahimtar komai da ke zagaye da ita a cikin gida.
Vicki ta ce, Flossie ba ta da sana’ar da ta wuce kwanciya tare da sharar bacci, ko kuma cin abinci mai dadi da ta saba samu.
A cewarta:
“Ba ta tsallake tayin abinci mai dadi ko kadan.”
Farin shigar Flossie kundin tarihi ya fara ne a watan Agustan 2022, lokacin da aka mika ta ga cibiyar kula da maguna ta Cat Protection a Burtaniya.
Wannan mage dai ta fara shiga hannun mutane ne a 1995, a lokacin da take karama tana gararanba a gari.
Ta sha sauyin iyayen gida, daga wannan hannu zuwa wannan har ta kai ga inda take a yau dinnan.
Bera ya samu lambar yabo a kasar waje
A wan labarin mai kama da almara, an ba wani bera lambar yabo bisa aiki tukuru da ba da gudunmawa a karkar tsaro.
Wannan bera ya yi ayyuka a wasu kasashen waje, inda yake taimakawa wajen gano inda aka dasa bam a kasa.
Mutane da dama sun ji mamakin irin aikin beran, kuma gashi aka bashi lambar yabo mai girma.
Source:LegitHausa