Wata mata a Kasar Amurka mai suna Dorothy Fedeli, ta auri kanta shekara 50 bayan mutuwar aurenta.
Matar ta ce “Na iya kokarina amma na kasa, to me ya sa ba zan auri kaina ba?” Kamar yadda ta fada kafin sanar da auren.
Dorothy Fedeli, mai shekaru 77, ta auri kanta ne a wani bikin iyali da aka yi jihar Ohio na Amurka.
Wani abin mamaki shi ne amaryar ta yi aure shekaru 50 da suka gabata, kuma bayan rabuwar auren ne, ta sha alwashin ba za ta ƙara aure ba.
Dorothy dai na da ‘ya’ya uku da kuma jika daya.
An ga matar sanye da fararen kaya tare da rike furanni a hannunta.
Daurin auren ya samu halartar ‘yan uwa da kuma abokai.
Ta ce ra’ayin auren kanta ya zo mata a lokacin da take cikin coci.
“Today.com” ta ruwaito cewa ta shafe shekaru 40 tana zama ita kadai, kuma ta yanke shawarar yin wani abu na musamman da kanta.
Fedeli ta ce tana cike da annashuwa kamar kowace amarya a ranar aurenta.
A wani labarin na daban matashiya ‘yar Nijeriya, Hilda Bassey Effiong da aka fi sani da Hilda Baci, ta zama sarauniyar dafa abinci ta duniya bayan da ta shiga gasar dafa abinci mafi tsawo wacce ta shafe kusan awa 100 tana dafe-dafen abinci kala-kala.
Hakan ya biyo bayan wani gasa ne da Guinness ta shirya ga duk wani ko wata da zai ko ta yi girki mafi tsawon lokaci ba tare da dakatawa ba.
Baci wacce ‘yar kasar Nijeriya ce mai shekara 27 a duniya, an haifeta ne a karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar Akwa Ibom, ta yi girki na tsawon sama da kwanaki hudu ba tare da zaunawa ba, inda ta dafa abinci kala-kala har sama da dari tare da rabar wa mutane kyauta.
Taken shiga gasar ta duniya shi ne ‘Dafa abinci cikin Kayyadadjen lokaci’. Ta fara girkin ne a ranar Alhamis makon jiya ta kammala ranar Litinin 15 ga Mayu, 2023 da yamma.
‘Yar Nijeriya da ta kafa tarihin nan a bangaren girki, Hilda Bassey Effiong, da aka fi sani da Hilda Baci, ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha wajen shiga a dama da ita da har ta samu nasara a bangaren dafa abinci wacce ta shafe tsawon awanni 100 tana girki.
Ta ce, ana gaf da karaya bayan shiga gasar, sannan, ta karar da dukkanin kuzarin jikinta da zai ba ta karfin guiwar cigaba, amma duk da hakan ta jure ta cigaba har sai da ta cimma nasara.
Ta ce, “Ina matukar godiya wa Allah. Na kusa sarewa a wannan gasar sa’o’i shida bayan da na fara a ranar Alhamis (Makon jiya), don na gaji kuma ba zan iya cigaba ba, amma mahaifiyata ta karfafeni ta kara min kumaji domin ta tsaya a tare da ni na tsawon awanni 14 hakan ya karfafa min guiwa matuka.
Ina kan wannan matakin nasarar ne saboda goyon bayanku da na mahaifiyata.
“Ina son na shaida muku dukkaninku cewa kowani irin mafarki na iya zama gaskiya, na shirya wannan samun wannan nasarar tun shekaru biyar da suka gabata, hakan ya zama cikin mafarkina, amma ban iya yin hakan wancan lokacin ba, amma yau ga shi na iya yi dukka saboda ku.
Ku nace kan mafarkinku wata rana zai zama gaskiya.”
Hilda Baci ‘My Food My Hilda’ ta lashe gasar dafa abinci na Guinness Book of Records, da ta shiga fagen dafa abinci na tsawon awa 100, lamarin da ya bai wa jama’a da dama mamaki matuka da farkar da dumbin matasa.
Masu kallon wannan al’amarin na ban mamaki da sha’awa na gasar abinci wanda aka nada a faifayin dauka, sun nuna bajintar Hilda a matsayin abun mamaki matuka gaya.
Hilda mai shekara 27, yanzu ta kafa babban tarihin wacce ta fi kowa jimawa a fagen dafa abinci.
Da take shelanta nasarar Baci na dafa abinci na tsawon awannni 96 zuwa 100 zuwa ranar Litinin din da ta gabata, babbar kawarta ta wallafa a shafin Instagram @ama_reginald cewa, “Baci ta kusan kaiwa awa 100 tana girki.”
Zuwa ranar Litnin da karfe 7:00pm, Baci ta kai awanni 99 a dakin dafa abinci, lamarin da ya kaita kwace ragamar wannan kambun a hannun wata ‘yar kasar India, Lata Tondon da ta zama tauraruwar dafa abinci na duniya a shekarar 2019.
Tata Tondon ‘yar kasar Indiya ce take rike da kambun bayan da ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 a shekarar 2019 tana girki.
Masu shirya gasar ‘Guiness World Record’ sun ce, kafin su amince da mutum ya samu nasarar sai ya gabatar musu da kwararan hujjojin lashe gasar da dukkanin matakan da aka gindaya.
Daga cikin abubuwan da ake alakari da su shine na farko mai bukatar shiga gasar zai gabatar da bukatar nuna sha’awar hakan da gabatar da kansa, zai/za ta yi girki na tsawon kwanaki 4 ba tsayawa; dole mai shiga gasar ya yi girki mafi tsawo ba tare da zaunawa ba, wanda ya fi yin girki na tsawon lokaci bai sare ba shine ke da kambun.
Kazalika, babu shan wasu kwayoyin kara kuzari ko na karfin jiki yayin shiga gasar ba; mai shiga gasar na da damar cin abinci, shan ruwa ko ruwan ‘ya’yan itace, da shan glucose.
Ita dai Baci ta shiga gasar ne daga wurin shakatawa na ‘Amore Gardens’ da ke Lekki, Jihar Legas, Nijeriya. ta yi girki safe da dare da rana na tsawon darare 4 ba tare da yin barci ba. Ta kan samu hutun minti 5 a kowani awa.
Ta na kwashe mintuna 30 a cikin motar asibiti da ke kusa da ita, inda za ta iya yin barci, ta yi amfani da dakin wanka, sannan ta sami tantancewar likita ko duba lafiyar ta daga tawagar likitoci.
Kazalika, duk abin da ta dafa tana raba wa mutanen da ke wurin kyauta ba tare da sayar da abincin ba. Ta kan dafa abinci daban-daban lokaci guda.
Tana da ‘yancin dafa duk abincin da take so. Babu takurawa kan girkin da ta iya da wanda ba ta iya ba.
Kowane abinci da aka dafa da kowane farantin da aka ba da shi ana rubuta shi. Ta dafa abinci sama da kala 115 kawo yanzu.
Kuma dukkanin yadda mai shiga gasar ya kasance to zai tura kai tsaye wa masu kula da gasar don haka ne ta kafa wannan tarihin.
Sai dai, masu shirya gasar sun ce, bayan mutum ya tura musu daukan hujjojinsa, to za su shafe tsawon mako 12 suna bibiya da tantance abubuwan da aka turo musu kafin daga bisani su amince da shi ko kin amincewa da shi.