Wani bidiyo mai daukar hankali ya nuna lokacin da wata karamar yarinya ke kallon iyayenta na sallah, sai ita ma ta fara binsu.
A cikin wannan bidiyo, yarinyar bata san ana daukarta ba a kamera, sai kawai ta fara bin yadda ake yin sallar kamar dama ta iya.
Karamar yarinyar ta daga hannayenta kamar mai addu’a kamar yadda musulmai da yawa ke yi a lokacin addu’a da kuma bayan sallah.
A rayuwar yara, suna koyon abubuwa da yawa ne daga kananan shekaru wajen iyaye da manyan da suka girme su; musamman dabi’un yau da kullum.
Yara na kuma koyo daga wasanni, don haka yake da kyau iyaye suke kulawa tare da daura yara kan turba ta gari don tsira duniya da lahira.
Wasu yaran kuma, basu cika maida hankali ga wasu abubuwan da ke da alaka da hankali da ma kawazuci ba a kananan shekaru.
Sau tari kamar wasa, yara kananan na koyon karatu da warware lissafi mai wahala wanda ke sanyawa su girma masu hazaka.