Gwamnatin babban birnin tarayya (FCTA) a ranar Juma’a a Abuja ta ba da tabbacin kare lafiyar mazauna yayin bukukuwan 12 na Yuni, ranar dimokiradiyya da zanga zanga da sauransu.
Babban sakatare na FCTA, Olusade Adesola, ya ba da tabbacin bayan taron kwamitin tsaro na babban birnin tarayya.
“Mazauna Abuja suna da son zaman lafiya. Don haka gaba daya mun himmatu ga yin bikin 12 ga Yuni na lumana, amma sakataren baiyi magana kan Zanga-Zangar da aka shirya gudanarwa a ranar ba.
Dangane da haka, hukumomin tsaronmu suna kan wannan alkawarin kuma sun tabbatar mana da cewa babu wani dutse da za a bari ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin mazauna ba,” in ji shi.
Ya ce, “hukumomin tsaro sun tsara wasu dabaru da za a yi amfani da su a wannan lokacin. Don haka, abu daya da zan iya fada wa mazauna yankin shi ne a ba su tabbacin tsaron su a cikin garin a tsawon wannan lokacin da ma bayan hakan.”
Adesola, saboda haka, ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da harkokin su na yau da kullum kuma na halal.
Game da satar mutane a yankin, sakataren ya ce, an yi yarjejeniya kan cewa ayyukan hadin gwiwar jami’an tsaro daban-daban zai gudana.
Ya bayyana cewa, FCTA na tallafa wa hukumomin tsaro daban-daban ta hanyar samar da karin motocin aiki da kuma dawo da wadanda suka lalace don bunkasa ayyukansu da kuma inganta lokacin amsa su.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar tsaro ta farin kaya da hukumar tsaro ta farin kaya sun ba da rahoto game da kafa runduna ta musamman don magance matsalar satar mutane a yankin.
Akan kalubalantar barace-barace akan tituna, wanda kuma yake haifar da barazanar tsaro ga mazauna Abuja, Adesola ya ce, za ayi amfani da hanyoyi da dama wadanda suka hada da wayar da kan mazauna kan hanyar da ta dace don yin sadaka.
“Mun kuma tattauna batun mabarata da suka shigo cikin gari kuma mun bullo da hanyoyin magance hakan da yawa. Misali, amfani da wayar da kan mutane don sanin cewa akwai ingantattun hanyoyin bayar da sadaka maimakon bayarwa ga wadanda ake kira talakawa akan tituna. Saboda ganinku da kuke baiwa talakawa akan tituna, zasu iya amfani da shi ta haramtacciyar hanya, za su iya amfani da shi don sayen kwayoyi,” in ji shi.