Kamar yadda tarihi ya tabbatar tsawon shekaru sama da dubu al’ummar musulmi mabiya tafarkin mazahabar ahlulbaiti wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a suke gudanar da ibadar tattakin ranar arba’in ta Imam Hussaini (S.A), wanda jikan annabi muhammad sallahau alaihi wa ahlihi wasallam ne, tarihi ya tabbatar da cewa zagayowar wannan rana tana da matukar muhimmanci ba ga ‘yan shi’a ba har ma ga mabiya tafarkin ahlussunah dama kiristoci.
Dogaro da littafan tarihin musulunci ta tabbata cewa Imam hussain ya gamu da ajalin sa ne yayin ga gamayyar sojojin yazid dan mu’awiyya suka tare shi a falalin filin karbala wanda yanzu gari ne a cikin kasar Iraki, inda suka kashe dukkan ‘ya’ya gami da mabiyan sa daga karshe kuma suka kashe shi ba tare da alamun imani ba, wannan rana ta ashura wacce akayi wannan ta’asa tana da matukar muhimmanci hakan ne ma ya sanya duk lokacin zagayowar ranar ake gudanar da zame zame na nuna juyayi a duk fadin kasashen duniya.
Bayan hakan a kan tuna zagayowar ranar arba’in da shahadar Imam hussain inda ake tattakawa daga gurare daba daban zuwa garin karbala wanda yanzu yake cikin kasar Iraki.
Miliyoyin mutane daga kasashen asiya turai dama afirka ne ke musharaka a wannan taron tattaki na Imam hussain wanda yake samun halartar muhimman mutane daga wadannan sassa na duniya gabaday.
Bincike ya tabbatar da cewa taron tattakin arba’in shine taro mafi yawan jama’a da ke gudanarwa a fadin duniya bhalin yanzu domin an tabbatar hatta taron hajji baya tara yawan mutanen dake taruwa domin tunawa da ranar zagayowar arba’in na Imam hussain (S.a).
Sai dai kuma abin takaici bullar annobar korona ta kawo tasgwaro mai matukar girma ga wannan ibada ta tattakin arba’in inda da dama aka hana su halartar wannan ibada sakamakon tsoron kamuwa da wanna cuta ta korona mai alamun ayar tambaya.