Jam’iyar Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ta madugun ‘yar adawa Marine Le Pen sun samu koma bayan a zagayen farko na zaben kana-nan hukumomi dake na ranar Lahadi wanda masu ra’ayin rikau ke ci gaba da samun nasara, a zaben da aka samu karancin fitowar jama’a.
Zabukan na jihohi da na kananan hukumomi na amtsayin zakaran gwajin dafi ga zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa – to sai dai karfe 8 na dare bayan rufe runfunar zabe, lamarin baiyiwa mahutanta a Fadar Elysee dadi ba.
Marine Le Pen ta masu tsattsauran ra’ayi da jam’iyyarta ta (RN) na fatan samun akalla mazabu 6 daga cikin manyan yankuna Mainland 13 na Faransa, to sai dai jiha daya tilo ta samu Cote d’Azur dake kudancin kasar.
Shugabar jam’iyyar masu tsattauran ra’ayi ta RN a Faransa Marine Le Pen.
Shugabar jam’iyyar masu tsattauran ra’ayi ta RN a Faransa Marine Le Pen. DENIS CHARLET AFP
Karancin fitowa
Kashi 26,72%, na wadanda suka cancanci kada kuri’u kadai suka samu fitowa zaben, wanda hakan ke nuna koma baya, idan aka kwantanta da zaben da ya gabata a shekarar 2015 da ya samu halartar kashi 40%.
Masharhanta dai sun fara bayyan fargabarsu kan matsalar da rashin halartar zaben da himma zai iya haifarawa wajen baiwa masu ra’ayin rikau nasarar lashe mafi yawan kujeru musaman a birnin Paris da kewaye.
Rashin halartar zaben da faransawan sukayi dai yana zaman babbar barazana ga tsarin gudanarwar kasar ta faransa, a yayin da Iraniyawa sukayi fitar farin dango a zaben da aka gudanar a ranar juma’ar data gabata.
A dai dai wannan lokaci kuma a kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma an gudanar da zabe cikin nasara tare da kalubalen da aka fuskanta daga kasashen ketare.
Zaben na Iran ya gudana cikin nasara kuma fiye da kaso hamsin cikin dari sun kada kuri’ar su, inda da dama suka bayyana goyon bayan su ga nizamin gwamnatin kasar duk da cewa bisa wasu dalilai basu samu damar kada kuri’a ba.
Masana lamuran siyasa suna ganin hakan ya nuna dimokoradiyyar kasar Iran tana kara samun babban cigaba sabanin kasashen yammacin turai irin su faransa inda kullum dimokoradiyya take samun tasgwaro da matsaloli.
A wani labarin na daban an kai hari kan helkwatar faransa dake mali, Majiyar France 24 tace harin wanda aka kaishi da mota makare da Bama-bamai a yankin Gossi dake tsakiyar kasar ta Mali ya haddasa raunuka.
Mutane dai a nahiyar afirka sun gajiya da zaman kasashen ketare a nahiyar musamman ingila da faransa.