Kamar yadda mai gabatar da kara a babbar kotun kasar ta gabon Ali Ogumba ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin sunyi yunkurin kifar gwamnati mai ci ta gabon wanda hakan ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin kasar kuma ya nemi kotun data tabbatar da hukunci mafi dacewa a kan wadanda ake zargin.
Sai dai a cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin a shekarar 2009 har da wasu ‘yan sanda inda mai gabatar da kara nakasar ta gabon ya bayyana ayyukan su a matsayin yima tsaron kasa zagon kasa kuma wanda ya zama wajibi a hukunta su bisa wannan babban laifin da suka aikata.
Babu jimawa dai a kasar mali ma sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula kuma suka karbi mulkin kasar ta karfin tsiya.
Yunkurin juyin mulki ya fara tsananta a kasashen afirka wanda masu lura da lamurrann yau da kullum suka alakanta hakan da matsin da shugabannin suke sanya mabiyan su a ciki.
A wani labarin kuma kasar isra’ila ta soki lamirin kama shugaban kungiyar ‘yan biyafara masu yunkurin ballewa daga kasar najeriya.
Kasar ta isra’ila ta shahara da tsomala baki a sabgogin da suka shafi najeriya wanda hakan ke zaman babbar barazana ga ‘yanzi gami da tsaron najeriya din.
”Idan isra’ila bata daina sanya baki a lamurran tsaron kasar mu ba a kwai babbar barazana ga tsaron kasa” kamar yadda wani mai lura da lamurran siyasa ya bayyana mana.
An dai tabbatar da kamun kanu ne bayan tserewa da yayi bayan kotu ta bayar da brlin sa kuma ya cigaba da tunzura mabiyan sa domin tada zaune tsaye.
Zuwa yanzu dai ba’a ga namdi kanu ko anji ta bakin ba, sa’annan lauyoyin sa da makusantan sa tun tabbatar da cewa hukumoni basu basu damar tattaunawa namdi kanu din ba.
Al’ummar najeriya suna kira ga gwamnatin najeriya da ta maida martani mai gauni kan wannan tsomala baki na haramtacciyar kasar isra’ila kan lamurran tsaron cikin gida na najeriya.