Rudunar ‘yan sandan jihar Kebbi, sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 66 a Kauyukan karamar hukumar Danko / wasagu da ke jihar ta Kebbi.
A watan Afrilu, ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda tara, daga cikinsu akwai DPO na ‘yan sanda na Danko / Wasagu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da kisan gillar da aka yi wa mutanen wanda ya faru a ranar Alhamis, inda aka gano gawarwakin mutanen da suka mutu a jiya a qauyuka takwas na karamar hukumar ta Danko/Wasugu.
A cewarsa, duk da cewa, ‘yan sanda na ci gaba da kirga yawan mutanen da suka mutu amma tuni rundunar’ yan sanda ta jihar ta tura jami’anta da jami’an ‘yan sandan karta kwana a waxannan kauyukan.
Kakakin rundunar, ya bayyana wa wakilin LEADERSHIP AYau ne yayin da yake zantawa da shi don jim ta bakin rundunar game da afkuwar lamarin. Inda a cikin bayaninsa ya tabbatar da faruwar hakan.
“Kisan ya faru ne a qauyukan Koro, kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge, duk a qaramar hukumar Danko / Wasagu ta jihar Kebbi, inji DSP Nafi’u Abubakar.”
LEADERSHIP AYau ta ruwaito cewa akasarin mutanen ƙauyukan da abin ya shafa sun tsere zuwa garin Ribah da ke kusa da su don kariyar rayuwarsu.
Kasar najeriya na fama matsalar tsaro amma gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaba muhammadu buhari maimakon fuskantar wannan babban kalubale ta bige da fada da kamfanin tuwita da facebook wanda hakan ke nuna sam gwamnatin bata damu da halin rashin tsaron da kasar ke ciki ba.
Gwamnatin najeriya dai ta shiga yakin kai tsaye da kamfanin tuwita inda ta sanar da haramta amfani da manhajar da tuwita a fadin kasar ta najeriya gabadaya.
An rawaito matar shugaban kasa ma ta goge shafin ta na tuwita kuma tana goyon bayan matakin da gwamnatin najeriyar ta dauka.