Daya daga cikin daliban makarantar Gwamnatin Tarayya ta FGC da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, da aka kai wa farmaki a ranar alhamis din makon da ya gabata, Muhammad Nasir Gugun- Sarki, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ‘yan bindiga suka kawo harin.
Haka nan ya bayyana wa wakilinmu yadda aka yi ya samu kubuta a yayin harin.
Ya fara da bayanin cewa, “Ni sunana Muhammad Nasir Gugun- Sarkina, ina aji biyu ne a makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri. A ranar alhamis dai ne da misalin karfe 10: 30 zuwa 11 na safiya, dalibai na rubuta jarrabawa, aka raba su uku don rubuta jarrabawar, wasu daga cikin daliban sun soma kammala rubuta jarabawar sun fito waje, wasu na wasa kuma na zaune, kamar ni da wasu abokaina bayan mun kammala rubuta jarabawar sai muka je dakin kwana muka canja kayan makaranta zuwa na wasa, muka wuce zuwa filin kwallo domin mu buga wasan kwallo.
“Bayan mun fara buga kwallon sai kawai muka fara jin harbin bindiga sau daya sau biyu tau! Daga nan fa sai muka fara tunanin me ke faruwa. Bayan ‘yan mintuna kawai sai muka ji ‘yan makaranta na kuwwa cewa ‘yan bindiga sun shigo makarantar, don akwai ‘yan makarantar firamare da kuma ‘yan Sakandare masu yin jeka ka-dawo, daga nan suka fara tattara dalibai suna sawa cikin motar da suka zo da ita da kuma bisa baburan da suka zo da su. ‘Yan bindigan sun fi mutum 200 da suka kawo hari a makarantarmu”. In ji dalibi Muhammad.
To ko ina jami’an tsaron da aka girke a makarantar suke a lokacin da aka kawo harin? Muhammad ya ba da amsa a ci gaba da jawabinsa, “Daga nan kuma ‘yan sandan ‘Mobile’ da aka girke a makarantar su 20 sun yi ta barin wuta da ‘yan bindigar kafin a kashe dan sanda daya. Ana cikin hakan wasu malamai suka rika daukar dalibai suna boye su a cikin gidajen makarantar.
Inda wani malami ya ce mani in zo mu shiga cikin gida, sai kawai wani dalibi ya ce wannan matsala ta fi gaban shiga gidan makaranta, kawai sai muka haura bangon makarantar ko da muke sauka sai muka yi ido biyu da wasu daga cikin ‘yan bindigar sai suka fara kiranmu cewa mu zo, daga nan sai muka fara gudu, muna cikin gudu sai na ga cewa bisa babur dinsu suke bin mu kawai sai na canja hanya na shige wani lungu, na ga wata itaciya sai na hau sama, wanda ya ba ni damar ganin duk abin da ke faruwa, ina cikin kallon abin da ke faruwa sai kawai na ga sun harbe yaro daya daga cikin wadanda muka fara gudu a tare.
“Bayan sun harbe shi ya fadi jini na zuba sai suka dauko shi bisa mashin dinsu zuwa cikin makaranta, kuma akwai ‘yan aji shida da za su dawo a ranar don rubuta jarabawar JAMB an zo daukarsu har sun fito Gate din makarantar sai ga ‘yan bindigar suka mayar da su cikin makaranta da sauran dalibai maza da mata da kuma wasu malamanmu suka tattara suka wuce da su.
Daga nan sai na ga sauran daliban da ba su samu sa’ar awon gaba da su ba, suna fitowa, sai ni ma na sauko bisa itaciyar na shigo makarantar, daga nan muka fara tafiya a kasa har zuwa kwanar shiga garin Yauri, sai na samu wani dan uwan babana ya dauko ni har zuwa gida.”
Ganin cewa Muhammad ya tsallaka rijiya da baya, wane hali ya tsinci kansa a gida?
Ya ce, “Bayan na shiga gida sai na yi wanka na ci abinci daga nan sai barci, bayan na tashi a lokacin ne hankalina ya dawo, sai na ba da labarin abin da ya faru a makarantarmu yadda mahara suka kawo hari har na kubuta. Wannan shi ne iya abin da zan iya fada”. In ji shi.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa akalla dalibai 88 ne ‘yan bindigan suka yi awon gaba da su a makarantar.
Babu makawa dai wannan hari ya taba zukatan yara daliban da abin ya shafa musamman wadanda suke can har yanzu a hannun ‘yan bindiga. Wannan ta sa Gwamnan Kebbi ya yi wani kukan kura a karshen makon da ya gabata na cewa zai jagoranci mafarauta da sauran jami’an tsaro su shiga daji domin ceto wadannan dalibai.
Kan haka, wakilin LEADERSHIP A Yau ya tattauna da wani masanin dabarun yaki da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga, Manjo Abdullahi Kwazo mai ritaya, inda ya yi karin haske kan yadda ake yi wa aikin tsaro rikon sakainiyar kashi a jihohin kasar nan.
A bayaninsa ya nunar da cewa, “a Jihar Kebbi akwai bukatar hadin kai tsakanin jihohin Kebbi, Sakkwato, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kuma Neja, saboda duk matsalar da Jihar Kebbi ke fuskanta Zamfara ce.
“Idan ana son magance wadannan matsalolin na ‘yan bindiga sai an ayyana wannan matakin da na fada. Haka kuma jami’an tsaro ne ya dace su jagoranci yaki da ‘yan bindiga ba ‘yan banga, ‘yan tauri ko maharba ba, domin akwai bukatar amfani da dabarun yaki, wanda ka ga jami’an tsaro su ne da ilimin dabarun yaki da duk wani dan ta’adda.
“Idan za a yi amfani da ‘yan banga, ‘yan tauri, maharba da sauransu ya zama wajibi su yi aiki a karkashin kulawar jami’an tsaro na ‘yan sanda ko na soji don gudun samun matsalolin na yawan kashe-kashen rayuka, saboda haka dokar ta bayyana.” In ji shi”.
Haka zalika ya ci gaba da bayyana cewa, “rashin bai wa jami’an tsaro kayan aiki wadatattu wata matsala ce mai janyo Yadda ‘yan bindiga na samun nasara kan jami’an tsaron kasarmu. Domin abin da ya faru a makarantar Birnin Yauri, rashin albarusai ne don albarusan nasu sun kare, amma na ‘yan bindigar sun fi na jami’an namu yawa, bayan albarusansu sun kare dole ne su yi gudun ceton rayuwarsu, ka ga ‘yan bindiga sun samu nasarar biyan bukatun su. Saboda haka mu gaya wa kanmu gaskiya idan har muna son wannan matsalar ta kare.”
Ya kara da cewa “tambayar da nake da ita ita ce ina ‘Air Defence’ namu suke ne da ake cewa jirgi na ta yawo a sararin samaniya? Kuma na ‘yan bindiga ne, har a kawo musu makamai, a kuma dauki wadanda suka samu rauni har a sanya su cikin jirgi amma duk Air Defence namu ba su iya ganin su ba, saboda haka akwai ayar tambaya a nan?.
“Wata matsalar kuma ita ce, ana samar da bayyanan sirri ga hukumomin tsaro, amma babu wani mataki da ake dauka a nan take, wanda wata matsala ce babba, mai kara barazana ga al’umma da kuma su jami’an tsaron namu.”
A cewar manjo Abdullahi Kwazo mai ritaya, akwai bukatar shugabanin jihohin kasar nan su cire son rai, su sanya mutanen da ke da kwarewa kan magance harakokin tsaro su jagorancin yaki da ‘yan bindigar, “ko kuma bai wa talakawan kasar nan dama su kare kansu da dukiyoyinsu ta hanyar doka, domin tura ta fara kai ga bango fa.” Ya bayyana.
Haka kuma ya shawarci gwamnatin Jihar Kebbi kan taron da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya yi da kungiyoyin ‘yan tauri, maharba da ‘yan banga da sauransu game da batun shiga daji ceto daliban.
“A matsayina na wanda yake da ilimi a kan dabarun magance matsalar tsaro, a yi amfani da jami’an tsaron sojoji ko na ‘yan sanda su jagoranci yaki da ‘yan bindigar da sauran wasu ‘yan ta’adda, Yadda ta hakan ne kai wa za a iya samun nasarar cafke su ko kuma a kashe na kashewa.
“Saboda idan ba a shinfida tsari maikyau ba za a iya samun abin da muke kira a turance ‘Reprisal attacks.’ Gwamnati na iya amfani da hanyar sulhu don ita wata hanya ce da ana iya samun nasarar dakile duk wannan hare-haren, sai in ta baci sai a yi amfani da karfin doka shi ne amfani da jami’an sojoji ko na ‘yan sanda.
“Saboda duk wanda ke shiga daji yana ganin irin yadda jirgi ke zuwa yana kawo musu makamai da albarusai kai har ma idan daya daga ‘yan bindigar ya samu rauni za ka an dauke shi a cikin jirgin, shi ma wata ayar tambaya ce, sanan sun fi jami’an tsaronmu makaman yaki na kwarai, ko abin da ya faru a Birnin Yauri albarusan sun fi yawa bisa ga na jami’an ‘yan sandan Mobile da aka kai a makarantar don samar da tsaro a wurin.” In ji shi.
Daga karshe Manjo Abdullahi Kwazo mai ritaya ya yi kira ga shugabannin kasar nan cewa su ji tsoron Allah domin jama’ar kasar nan sun zabe su ne domin yi musu kyakkyawan shugabanci.