Shekarar 2023 ake cika shekaru uku da shahadar babban kwamandan rundunar kare juyi juya halin musulunci na Jamhuriyar Muslunci Ta Iran, a Najeriya masoyan kwamandan sun gudanar a tarukan tunawa da wannan rana.
An gabatar da wadannan tarukan a garuruwa mabamban ta ciki har da babban birnin tarayyar Abuja da kuma kano.
A kano kamar ya yadda ya gabata wannan shine karo na uku da ake gudanar da wannan taro kuma taron ya samu halartar malamai da masana da sassa daban daban.
Malamai sun gabatar da jawabai masu muhimmanc dangane da falalar shahada gami da matsayin shahidai a tafarkin Allah ta’ala.
Sa’annan malaman sun kore shubuhohi wadanda wadandu marasa tsoron Allah suke yadawa dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Irann da kuma Kasim Sulaimani musamman dalilin shahdar sa da kuma dalilan da sula sanya Amurka tayi kwance kwance ta harbawa motarsa mizayin a bagaadaza babban birnin Iraqi.
Shi dai Kasim sulaimani shine babban kwamandan rundunar “”Qods Force” wacce gwamanatin Iran ta kafa kuma ta bata alhakin fada da ta’addanci a gabas ta tsakiya.
Sojojin Amurka bisa umarnin shugaban kasar na lokacin Donald Trump sun shammaci kasm sulaimani yayin da yakai ziyarar aiki bisa gayyatar da gwamnatin kasar Iraki tayi masa, inda sojin na Amurka suka harbi tawagar motocin sa da mizayil kuma take suka konesu kurmus.
Me yasa Amurka ta kashe Kasim Sulaimani?
Bayan kisan Kasim Sulaimani gwamnatin Iran ta bayyana hakan a matsayin babban abin takaici kuma ta bayyana dalilin wannan kisan yadda Kasim Sulaimanin ya hana Amurka rawar gaban hantsi a yankin gabas ta tsakiyan.
Duniya ta bayyana Kasim Sulamani a matsayin gwarzon bada kariya ga raunana da masu neman taimako musamman a yankin daya fito na gabas ta tsakiya.
‘Yan gwagwarmaya masu fafutukar neman ‘yanci a fadin duniya suna gudanar da tarukan tunawa da Kasim Sulaimani domin tunawa dashi a matsayin gwarzo.