Tirkashi lallai gaskiya bata buya Allah ya bayyanar da gaskiya a wani sabon karatu da babban malamin nan wanda ya shahara da kare martabar annabi (s.a.w) ya bayyana yana bada amsoshi kuma gamsassu dangane da mukabalar wasan kwaikwayo wanda akan gabatar ranar asabar din data gabata.
Kamar yadda ta bayyana ana iya cewa malaman maja na kano murna ta koma ciki domin malamin ya bayyanar da yadda aka titsiye shi aka hana shi ‘yancin da yake dashi, sa’annan kuma aka sanya yaudara da magu magu kamar yadda malamin ya tabbatar.
Malamin ya tabbatar da cewa kamar an sanya shi a garken zakuna da kuraye ne saboda haka bashi da ikon gabatar da kowanne bayani domin dama an tsara ne a titsiye shi kuma a bayyanawa duniya cewa an kure shi.
Mabiya malamin sun nunfasa inda suka fara bayyana suna nuna godiyar su ga Allah ta’ala bisa wannan sassauci da aka samu bisa halin da suka shiga.
Kamar dai yadda shehin malamin ya bayyana zai cigaba da warware dukkan matsalolin kuma zai ke bada amsoshin tambayoyin da aka kaishi kara wajen gwaamnati cikin nutsuwa da yalwar lokaci kamar yadda ya bukata amma aka hana shi saboda yaudara kamar yadda ya bayyana.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lallai an shirya duk mai yiwuwa domin cin zarafin malamin da kuma tabbatar da cewa bai iya katabus ba a wajen mukabalar amma abin mamaki da malamin ya samu nutsuwa ya zauna ya warware mafi yawanci daga cikin matsalolin kuma Alhamdulillah gaskiya ta fara bayyana.
Zuwa yanzu dai magana tana gaban kotu saboda haka babu wanda yake da ikon taba malamin har sai kotu ta tabbatar da hukunci kuma lauyoyin malamin suna cigaba da bibiyar lamarin.
Ga mai bukatar saurarar bayanan malamin wadanda ya fara gabatarwa ranar 13/7/2021 yana iya bincikar inda ake samun bayanan malamin a zaurukan whatssapp da sauran su.
Tirkashi, Allah dai shi kyauta kuma kuma Allah shiryi malamain masu sanya yaudara da cin amanar ilimi cikin sabgogin su, shi kuma malama Abduljabbar Alllah bashi kariya ta musamman.