Kamar yadda ministan harkokin wajen syria Faisal Mekdad ya bayyana yayin zaman wakilan majalisar duniya (UN), ya tabbatar da cewa gwamnatin syria karkashin jagorancin shugaba Bashar AL-assad tana da kowacce irin dama domin kwato tuddan golan tare da dawo dasu karkashin ikon ta kuma hakan bai sabawa kowanne tanadi na dokokin kasa da kasa ba.
Ministan ya tabbatar da cewa tuddan golan wanda haramtacciyar kasar isra’ila ta mamaye shekaru da suka gabata har yanzu suna cikin lissafin iyakan kasar ta syria kuma a koyaushe gwamnati shugaba bashar Al-assad taso tana iya kwato su gami da maida su cikin ikon ta.
Kasar syria dai tana cikin kasashen da suke fama da mamayar yahudawan haramtacciyar kasar isra’ila.
An samu matsaloli da suka hada da yake yake tsakanin gwamnatin shugaba nbashar AL=assad da kuma sojojin baki ‘yan share wuri zauna masu samun goyon bayan kasar amurka da turawan yamma.
Ba dai a jima da gabatar da zabe ba a nkasar ta siriya inda shugaba mai ci Bashar Al-assad ya kuma lashe zabe inda ajawabin sa na karbar mulki a wannan karon ya tabbatar da karin kokari domin tattabatar da ‘yanci gami da tsaron rayuwa da lafiyar al’ummar siriya.
Ana iya cewa matakin shugaban na siriya baizo da mamaki ba domin dama tun asali yankin tuddan golan ya kasance kasar siriya ne kafin sojojin haramtacciyar kasar isra’ila su mamaye yankin.
Haramtacciyar kasar isra’ila ta shahara da mamayar kasashe dake makotaka da ita wanda suka hada da siriya din.
Ana dai ta samun rikice rikice wanda basa rasa nasaba da kokarin yahudawan na haramtacciyar kasar isra’ila domin mamaye wasu karin wuraren a cikin kasar falasdinu.
Yakin kwanaki 12 wanda aka gudanar a azumin daya gabata shine babban rikicin da aka shaida a baya bayan nan kuma ya dauki hankalin al’ummar duniya amma har zuwa yanzu sojojin haramtacciyar kasar isra’ila suna kashe falasdinawa dama sauran kasashen makota irin su siriya da labanon da sauran su.