Jihar boronon arewacin najeriya ta jima da zama sansanin ‘yan tada kayar baya masu kokarin tada hankalin mutane gami da aikata ayyukan ta’addanci, tun wancan lokaci da kungiyar ta’addanci nan mai rajin kafa gwamnatin wahabiyanci ta bulla a garin na maiduguri gwamnatin najeriya ta fara tura sojoji na musmman jihar domin tattabatar da cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta barno amma abin takaici har zuwa yau ba’a samu zaman lafiya ajihar ba.
Da safiyar yau ma dai sojoji ne wadanda aka kai jihar domin samar da zaman lafiya sukayi baje kojin wasu kayayyaki da suka samu bayan sun tashi wani babban sansanin ‘yan tada kayar baya masu akidar wahabiyanci a jihar barnon.
Kayan wadanda suka hada da mota, keke, magungunan kara karfin jima’i na cikin kayyayakin da aka samu a maboyar ‘yan tada kayar bayan.
Rundunar sojoji mai yaki da ta’addanci a yankin na maiduguri na bataliya ta 195 sector 1, ”OPERASHIN HADIN KAI” sune suna aiwatar da wannan atisayen na tashin maboyar ‘yan ta’addan kuma suka bayyanawa manema labarai abubuwan da suke samu a hannun ‘yan ta’addan.
Kwanakin baya an jiyo gwamann jihar da borno farfesa zulum yana tabbatar da cewa baya tsoron zuwa ko’ina a fadin jihar tasa amma ana kallon hakan a matsayin hadari babba ga rayuwar gwamnan domin zuwa yanzu a kwai sassa da dama a jihar ta maiduguri da kungiyar ta’addanci ke iko dasu.
Hasalin bullar ta’addanci dai a garin maiduguri ya samo asali ne daga bullar kungiyar boko haram mai akidar ahlussunnah kuma mai da’awar wahabiyanci, wanda daga wancan lokaci zuwa yanzu garin maiduguri dama sauran garuruwan jihar borno yayi bankwana da zaman lafiya.
Gwamnatin najeriya ta sha alwashin gwamawa da kungiyar wahabiyancin ta boko haram amma daga baya sai a ji sun kara bulla ba ter da sassaci ba.
Wani mai lura da lamuran yau da kullum ya bayyana masa cewa dole sai an murkushe birbishin akidar wahabiyanci a cikin al’umma sa’annan za’a samu zaman lafiya.