Shugabar Tanzania ta dage hanin yakin neman zabe
Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta janye wata dokar hana gudanar da gangamin yakin neman zane da tsohon shugaban kasar mai ra’ayin rikau John Magafuli ya kafa shekaru shida da suka gabata.
Ta ce wannan shawarar da ta yanke na karskashin wani shirin hada kai da sake gina kasar ne mai suna 4R.
Ta lura cewa jam’iyyun siyasa a kasar na da ‘yancin gudanar da yakin neman zabensu sai dai ta bukace su da su guji zagin juna kana su kasance masu mutunta juna. Toshon shugaba Magafuli ne ya kafa dokar hana jam’iyyun gudanar da gangamin yakin neman zabe, matakin da wasu ke kallo a matsayin rage karfin da jam’iyyun ke da shi.
Ta sanar da matakin ne yayin wani taro da ta kira tare da manyan jami’an da ke jagorantar jam’iyyun siyasa.
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Chadema a kasar Freeman Mbowe ya yi maraba da matakin.
Ya ce matakin farko shi ne mayar da dukkan ‘ytancin da ‘yan kasar ke da su kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
Shugaba Samia ta kuma yi alkawarin duba wasu bukatu da jam’iyyun suka dade suna kokawa kansu.
Ita ce jagorar jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), wadda ta shafe fiye da shekara 50 tana mulkin kasar.