Kamar yadda kafar sadarwa mallakin jamhuriyar musulunci ta Iran mai suna Fars News ta wallafa a shafin ta na tuwita, yau ne Iraniyawa suke zaman makomkin cika shekaru talatin da uku cif domin tunawa da kisan iraniyawa dari shidda da hamsin da biyar da sojojin amurka sukayi a tekun farisa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shekaru talatin da shidda da suna gabata sojojin amurkan sun harbo wani jirgin fasinja wanda yake dakon iraniyawan kuma an tabbatar da cewa iraniyawa dari shidda da da hamsin da biyar ne suka rasa rayukan su a dalilin wannan hari da sojojin na amurka suna kai a kan jirgin fasinjan mallakin jamhuriyar musulunci ta Iran.
Abin lura sojojin na amurka sun harbo jirgin wanda mallakin jamhuriyar musulunci ta Iran ne kuma a ruwan tekun farisa wanda shima mallakin Iran din ne, amma babban abinda yafi zama abin takaici ga Iraniyawan shine zuwa yanzu amurkan bata bada uzuri danagne da wannan lamari ba balle kuma ta nemi afuwa ko ayi batun biyan diyyar asarar rayuka da duniya da akayi sakamakon harin na sojojin amurkan.
Shugaban kasar Iran mai barin gado hassan rouhani ya jaddada takaicin sa dangane da halayen rashin kyautawa na amurkan a yankin gabas ta tsakiya inda ya bayyana amurka a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar yankin na gabas ta tsakiya.
Hakanan ministan harkokin wajen Iran javad zarif ya wallafa a shafin sa na tuwita inda ya bayyana harin kan Iraniyawa a shekaru talatin da uku da suka wuce a matsayin keta haddin dan adama.
Javad zarif yace ya shaidu lokacin ne sannan yana matsashin ma’aikacin diflomasiyya sa’annan lamarin ya bashi mamaki gami da takaici matuka yadda amurkan ta kekasa kasa taki ko da neman afuwar Iraniyawan bisa wannan babban laifi data aikata musu.
Bisa al’ada dai duk shekara idan ranar ta zagayo iraniyawa suka je tekun na farisa inda lamarin ya faru domin gudanar da zaman makoki da kuma tunawa da shahidan da wannan lamari ya rutsa dasu.