Shanu Sun Fi Man Fetur Da Iskar Gas Daraja, In Ji Adamu Garba.
Adamu Garba, tsohon mai neman takarar shugaban kasa ya ce shanu sun fi man fetur da iskar gas daraja.
Garba ya bayyana hakan ne yayin da ya ke martani kan umurnin da gwamnonin yankunan kudu suka bawa fulani na barin arewa.
A cewarsa kudaden da za a rika samu daga madara da kiwon shanu da nama ya fi kudaden da gwamnati ke bawa jihohi Tsohon mai neman takarar shugaban kasa Adamu Garba ya ce shanu sun fi dukkan man fetur da iskan gas da ke kudancin Nigeria daraja, The Punch ta ruwaito.
Garba ya bayyana hakan ne yayin da ya ke martani kan shawarar da kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders’ Association of Nigeria, MACBAN, reshen jihar Bauchi ta bawa mambobinta na cewa su bar jihohin kudancin 17 a kasar.
MACBAN ta bada shawarar ne bayan gwamnonin jihohin kudu sun sanar da cewa sun haramta kiwo a yankin kudu bayan taron da suka yi a Asaba, babban jihar Delta.
A martaninsa a Twitter, “Na yarda da wannan umurnin. Dukkan fulanin da ke kudancin Nigeria su dawo.
Za mu yi amfani da shanu da abubuwan suke samarwa mu rika siyarwa kasashen duniya. “Shanu ya fi man fetur da iskar gas da muke da shi gaba daya a Nigeria.
Ya kamata masu ruwa da tsaki a arewa su dauki kiwon shanu a matsayin sana’a ba wai al’adda ba kawai su kuma saka hannun jari #CowToCurrency.
Shanu kadai sun isa su warware matsalolin arewa.”Litar madarar shanu a N350 ya fi litar mai a N145.
Idan muna da shanu miliyan 20, idan aka dauki misali shanu na samar da madara lita 5 a kowanne rana, za mu samu kimanin Naira biliyan 2 a kowanne rana. Hakan na nufin kimain Miliyan 700 a kowanne jiha a kowanne rana.
Kimanin Naira Biliyan 21 a jiha a wata daya. “Wannan adadin kudin ya fi kason da jihar arewa mafi samun kudi mai tsoka daga gwamnatin tarayya ke samu a wata. Kuma, kowanne shanu na samar da ayyuka 3. Kiwo, Yanka, Gyara, Tallatawa, Sayarwa da Kula da Nama.
Shanu miliyan 5 za su samar da ayyuka miliyan 15. Ina mamakin son jiki na gwamnonin arewa.
A wani labarin daban, jami’an yan sanda sun halaka a kalla yan ta’addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata,
PRNigeria ta ruwaito. Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta’addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan.
‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri. Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta’addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.