Kamar yadda kafar sadarawa ta Press T.v ta tabbatar a kwai yiwuwar shugaban kungiyar fafutukar tabbatar da ‘yancin kasar labanon dinnan watau sayyid hassan nasrullah zai gabatar da jawabin kai tsaye wanda za’a za’a watsa a gidajen talabijin masu alaka da bangaren ‘yan gwagwarmaya.
Shugaban na hisbullah zai gabatar da jawabin ne daga babbar birnin kasar labanon watau beirut kuma ana sa ran zai tabo manyan batutuwa da suka shafi tsaron yankin gabas ta tsakiya dama lamurran falasdinawa.
Bayanan shugaban na hisbullah suna zuwa ne a dai dai lokacin da aka samu canjin gwamnati a haramtacciyar kasar isra’ila kuma aka samu nasara a kan isra’ilan a yakin kwana goma sha biyu da aka gudanar tsakanin falasdinawa da sojojin haramtacciyar kasar isra’ila.
A bisa al’ada bayanan sayyid hassan nasarullah kan yi matukar tasiri a yankin gabas ta tsakiya dama duniya baki daya musamman a kasa labanon da kuma makociyar ta falesdinu amma sai dai bayanan na nasrullah kan fito da tsantsar rushe shirin yahudawan haramtacciyar kasar isra’ila wacce take matsayin ‘yan share wuri zauna a yankunan kasar falasdinu.
A wani labarin na daban kungiyar ceton al’ummar falasdinu ta Hamas tayi maraba da matakin wasu daga cikin yahudawa ‘yan share wuri zauna ba barin gabar tekun ”west bank” bangaren unguwar nablus kungiyar ta hamas ta bayyana matakin da yahudawan suka dauka na barin gabar kogin a matsayin ganin uwar bari da sukayi kuma hakan yadda tabbatar da karfin da kungiyar kare hakkin falasdinawan tayi na tabbatar da cewa makiya sun bar sansanonin gudun hijirar da suka mamaye.
Kungiyar ta hamas ta tabbatar da cewa da yardar Allah yahudawan sum kusa barin kasar falasdinu ko suna so ko basa so domin falasdinu da maasallachin kudus na musulmi ne kuma falasdinawa.
Yankin falasdinu dai yana fama da matsalolin yahudawan sahayoniya ‘yan share wuri zauna wadanda ke tafka zalunci a kan raunanan falasdinawa tsawon shekaru.