Kamar yadda kotun dake sauraron shari’ar sheikh ibrahim zakzaky ta tabbatar a wancan zaman, za’a cigaba sa sauraron karar da gwamanatin jihar kaduna ta shigar da babban malamin da mai dakin sa ne ranar ashirin da takwas ga wannan watan na yuli da muke ciki. ma’ana sauran kwana biyu kenan.
Idan ba’a mance a zaman daya gabata lauyoyin malam zakzaky sun gabatar da bukatar kotu ta kori wannan kara domin bata da makama balle tushe kuma ma shaidun da masu kara suka gabatar sun kasa alakan ta malamin dko mai dakin sa da laifin da ake tuhumar su dashi wanda hakan yake nuna bangaren masu kara kurum suna batawa wanda ake kara lokaci ne kuma tare da cewa yana fama da rashin lafiya wanda yake bukatar fita waje domin kula da lafiya.
Sai dai sauran bangaren lauyoyin gwamnatin jihar kaduna sun dage a kan cewa lallai sai kotu ta saurari karar tasu duk da rashin gabatar da wadatattun shaidu da sukayi.
An dai jiyo daya daga cikin lauyoyin sheikh zakzaky, barista ishaq adam yana cewa a yadda shari’ar take gudana indai za’a bi ka’idar da kuma al’adar shari’a ne lallai kotu bata da wani hukunci ta zata yanke illah ta saki malam zakzaky domin duk shaidu sun tabbatar da cewa bangaren masu kara basu iya gabatar da wata gamsashshiyar hujja wacce ta alakanta malamin ko mai dakin sa da laifukan da ake ikirarin tuhumar su dasu ba.
Sai dai a tattaunawar mu da daya daga cikin mambobin harkar musulunci din ya tabbatar mana da cewa su basu tsammanin gwamnatin nasir el-rufa’i zatayi musu adalchi saboda haka sun mika al’amuran su ga Allah ta’ala domin sun tabbatar gwamnatin zatayi duk mai yiwuwa domin dai ta tabbatar ba’a saki malamin ba kuma koda kotu ta sake shi ma gwamnatin tana iya kunnen uwar shegu da hukuncin kotun kamar yadda gwamnatin tarayya ma tayi kunnen uwar shegu da hukuncin babbar kotun tarayya wacce ta wanke shaihin malamin da mai dakin sa kuma tace a biya su naira miliyan hamsin domin diyyar bata musu lokaci gami da bata musu suna da akayi ba tare da sun aikata laifin komi ba.
An dai zura idanu ana jira, sauran lamari sai ranar 28 idan an kammala shari’ar za’a tabbatar.