Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana cewa ta aika da wani kwamitit na sanatoci zuwa Ingila domin aiki dangane da kamun da aka yima tsohon mataimakin shugaban majalisar mista Ekweremadu da matar sa bisa zrgin safarar dan adam gami da cirar sassan mutane.
Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar sirri da sanatocin sukayi, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa wasu manyan sanatoci gami da kwamitin harkokin kasashen wajen majalisar dattawa karkashin jagorancin sanata Adamu Bulkacuwa zasu tafi Ingilan kuma zasu hada kai da ofishin jakadancin Najeriya dake Ingilan domin bincike kan musabbabin lamarin gami da laluben bakin zare.
Sanata Ahmad ya bayyana cewa a karan kan sa zai cigaba da tuntubar ambasadan Najeriya a londan Ambasada Ishola Sarafa kuma ya tabbatar da cewa majalisar dattawa zata cigaba da bibiyar lamarin cire sassan jikin dan adam wanda ake zarginabokin aikin nasu sanata Ikweremadu din.
Matsayar majalisar dattawan dai tana zuwa ne bayan wani kuduri d aka gabatar dangane da kame tsohon mataimakin shugaban majalisar da akayi a kasar Ingila bisa zargin sa da cire sassan jikin bil’adama.
A wani labarin na daban biyo bayan kame sanata Ikweremadu gami da zargin sa da safarar dan adam gami da zargin cire sassan dan adam reshen jam’iyyar PDP ta Inugu ta gabas ta rubuta wasika zuwa bangaren bada bisa na embasi din Ingila dake Abuja inda take bayyana wanene yaron da ake zargin Ikweremadu ya sace.
Sabbin bayanan da suke fitowa dangane kamun sanatan da matar sa Beatrice, suna tabbatar da cewa, tsohon mataimakin shugaban majalisar datatwan ya rubuta takarda ga bangaren bada bisa na ofishin ambadan Ingila dake Abuja cewa, yana bukatar a gaggauta bada bizar yaron wanda yanzu ake zargin Ekweremadu ya tafi dashi ne domin cire hantar da domin a sanyawa ‘yarsa wacce ke fama da rashin lafiya.
Wasu bayanan dai sun tabbatar da cewa hatta majalisar datawa karkashin Jagorancin Ahmad Lawan ma ta shiga maganar, zamu kawo muku rahoton majalisar a rahoto na gaba.