Hukumar nan kula da ayyukan man fetur ta najeriya NNPC ta bayyana cewa ya kamata arika sayar da litar man fetur sama da naira dari biyu da tamanin sabanin yadda ake sayarwa a halin yanzu.
Gwamnatin najeriya ta jima tana da burin daga farashin man fetur amma hakan yana gamuwa fushin ‘yan najeriya wanda hakan ya kawo jan kafa a kudurin da gwamnatin ta najeriya ta jima dashi.
”’Yan najeriya suna cikin wani halin matsin tattalin arziki da rashin tsaro tattare da hakan gwamnati na shirin kara farashin man fetur wannan rashin adalchi ne” a ta bakin wani direban ada i dai ta sahu da muka samu tattaunawa dashi a jihar kanon arewacin najeriya.
Zuwa yanzu ana jira aji ta bakin kungiyar kwadago ta najeriya dangane da ikirarin hukumar NNPC domin kungiyar ta kwadago itace a sahun gaba wajen yaki da kara farashin man fetur din.
Najeriya tana cikin kasashen afrika ta yamma dake fama da matsalar Boko Haram, matsalar masu garkuwa da mutane da kuma masu satar shanu.
A bangare guda ga mabiya darikar shi’a nata jerin gwanon lumana akullum sakamakon rike shugaban su da gwamanati tayi.
A wani labarin na daban hukumar DSS ta hana lauyan shugaban ‘yan biayafara Namdi Knu gani sa a inda ake tsare dashi.
Gwamnatin ta najeriya ta cafke namdi kamu ne a cikin wannan satin yayin da ministan shari’a na najeriya barrista malami ya tabbatar da kamun namdi kanu din.
Majiya ta kusa da Namdi kanu ta tabbatar da cewa ya shiga hannun jami’an tsaro amma abin takaici hukumar DSS din ta killace shi sama da awa ashirin da hudu ba tare da ta barilauyan sa ya ganshi ba balle kuma iyali da ‘yan uwan shugaban na kungiyar IPOB mai kokarin ballewa daga tarayyar najeriya gami kama sabuwar kasa ta ‘yan asalin kudu maso gabas din najeriya.