Fiye da shekaru 400 da suka gabata duniya ta shaidi abinda ake kira da safarar bayi, safarar bayi tayi babban tasirin da bata taba yi ba a hanyar afirka zuwa turai.
Masara tarihi sun tabbatar da cewa tarihi ya sajjala wani bakin lamari wanda ya zama abin takaici a tsawon zamunna kuma ak samar da tabon da har karshen duniya ba za’a iya goge shi ba.
Tabbas turawan yammacin turai sun zalunci ‘yan asalin afirka bakaken fata wadanda suka dinga safarar su daga nahiyar afirka zuwa turai domin yin ayyukan kaskanci gami da tozarci.
A zahirin gaskiya bature bai dauki bakar fata a matsayin cikakken mutum ba wannan ma tasa bature ya raina bakar fata matuka gaya kuma duk lokacin daya samu dama zai wulakanta bakar fata wanda hakan ne ya faru a tarihin safarar bayi daga afirka zuwa yammacin turai.
A yau sakamakon wasu dalilai turawa suna kokarin boyewa ko kuma goge wancan bakin tarihi na safarar bayi amma hakan bazai yiwu ba domin alkaluman tarihi sun jima da sajjala bakin zaluncin da turawan suka aiwatar a kan bakaken fata.
Da yawa cikin bakaken fatan da aka diba zuwa turai da sunan bayi sun rasa rayukan su ne a hanya, wasu idan yunwa da rashin kulawa ya tsananta musu suka kamu da rashin lafiya bature baya da lokacin yi musu magani, hakanan zai dauko su ya cilla cikin teku.
Bakaken fata sun tsinci kansu a sabuwar duniya inda basu san kowa ba, basu da dangin uwa balle na uba kuma a hakan an kaisu turai ne a matsayi bayi wulakantattu wanda karen bature ko yanwar sa ta fisu daraja da mukami.
Zuwa yau bakaken fata wadanda suke rayuwa a turai zasu tabbatar maka da cewa wariyar launin fata gami da zaluntar bakaken fata bai ragu ba a nahiyar turai kusan sai ma abinda ya karu.