Bayan gabatar da zabe a jamhuriyar musulunci ta Iran inda ‘yan takara hudu suka nemi kujerar shugabancin kasar kuma sakamakon zabe ya fito da Sayyid Ibrahim Ra’isi a matsayin wanda ya lashe zabne da kaso mafi yawa kuma a matsayin sabon shugaban kasar ta jamhuriyar musulunci ta Iran.
Kamar yadda yake kundin tsarin mulkin kasar ta jamhuriyar musulunci ta Iran kowanne sabon shugaban kasa yakan kama aiki ne bayan kwanaki 45 bayan zabne sa matsayin shugaban kasa.
A wannan rahoton zamu tabo batutuwan da suke da alka da sabon shugaban kasar Iran din a lokacin da yake zaman jiran ranar da za’a rantsar dashi kuma a mika masa ragamar shugabancin kasar inda zai kama aiki gadan gadan domin fuskantar tarin matsalolin da suke damun iraniyawan wanda suka hada da matsin tattalin arziki sakamkon takunkuman tattalin arziki daamurka ta kakabawa gwamnatin data gabata ta shugaba hasssan rohani.
Sabon shuganam kasar Iran sayyid ibrahim ra’isi wanda iranayawa ke ma kallon wanda yazo ya ceto su daga hannun masu ra’ayin dogara da yammacin turai domin samar da yanayin samun morewa rayuwa.
Sabon shugaban wanda yake daga cikin na kusa kusa da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Aali Khamene’i ana sa ran zaiyi aiki bisa ka’ida tare da jagoran domin maganin matsalolin da suka addabi iraniyawan.
Tun da jimawa dai jagoran addinin na Iran ya bama gwamnatin kasar shawara da cewa ta cire tsammani daga taimakon turawan yamma domin babu abinda turawan na yamma ke kaiwa duk kasar da suka shiga illah rashin tsaro, matsalolin tattalin arziki da dai sauran su.
Ana sa ran idan sabon shugaban kasar na Iran ya karbi aiki zai aiwatar da shawarwarin jagoran addinin na kasar ya jima da wallafawa wanda ake sa ran nhakan zai bude hanyar samun mafita daga tulin matsalolin da suka addabi iraniyawan wanda aka ta’allaka hakan da kin bin shawarin jagoran addinin kasar da gwamnatin data gabata tayi.