Gwamnatin jihar Gombe a ranar Litnin ta sanar da cewa rikicin kabilanci tsakanin Shongom da Faliya kan filin gona ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da kona gidaje akalla 50.
Kwamishanan labaran jihar, Julius Ishaya, ya sanar da hakan a hira da manema labarai bayan zaman majalisar tsaro na Gombe, rahoton Vanguard.
A jawabinsa, ya ce rikicin ya auku ne ranar Asabar, 29 ga Mayu kuma wata mata ta rasa rayuwarta. “Majalisar tsaro ta jaddada haramta ayyukan yan banga da kungiyoyin mafarauta kuma an sanar da dukkan hukumomin tsaro kan haka,” yace.
Ya ce gwamnatin jihar ta umurci shugabannin gargajiyan garuruwan su gana da matasansu domin takaita wannan rikici. Rikicin kabila ya sake barkewa a Gombe, an kona gidaje akalla 50 Source: UGC Hakazalika kwamishanan tsaro na jihar, Adamu Dishi, ya ce kurar ta kwanta yanzu.
Ya ce an umurci jami’an tsaro su fito da wadanda suka haddasa wannan rikici, saboda rikici ba ta barkewa da kanta kuma wajibi ne a hukuntasu. Kwamishanan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai NAN wannan labari na rikici tsakanin Shongom da Filiya.
Ya tabbatar da cewa an kona akalla gidaje 50 kuma an hallaka mutum daya.
Ya ce za’a hukunta dukkan wadanda ke da hannu cikin wannan rikici bayan kammala bincike.
Rikicin kabilanci dai ya zama babbar barazana a arewacin najeriya inda yaci rayukan mutane da dama, wani abu da wakilan mu suka binciko shine, rikicin na kabilanci ya kuma yi kamara a kudancin najeriya ma wanda hakan yake barazana ga kasar ta najeriya.
Gwamnatoci ake sa rai su kawo karshen irin wadannan rikice rikicen amma dai kamar a yadda lamurra suke nunawa gwamnatoci sun kasa kawo kashe matsalar tsaro ma balle matsalolin kabilanci a kasar ta najeriya mai yawan al’umma da yaruka gami da kabiloli da daman gasaken gaske.
Masu karatu mene ra’ayoyin ku dangane da rikicin kabilanci a kasar mu ta gado Najeriya?
Sai ku bayyana mana a sashen comment.