Biyo bayan nasarar da gamayyar malaman da aka sanya ma suna da ”Malaman Maja” sukayi a kan sheikh Abduljabbar inda har ta kai ga cewa sunyi sanadiyyar hukumomi suka kama shehin malamin kuma a halin yanzu yake gidan kaso kuma yana fuskantar shari’a a ranar 28 ga wannan wata na yuli da muke ciki, abin mamaki tun ba’a je ko’ina ba gayyar ‘yan majan ta ruguje domin kalaman da suke fitowa daga bakunan malaman na nuni da cewa lallai babban rikici ya balle a tsakanin su wanda kuma yake nuna dama an hadu ne domin son zuciya da kuma yakar sheikh Abduljabbar dinne domin son zuciya ba domin bada kariya ga manzon Allah (s.a.w.w)
ba.
Tun da farko shehin malamin nan na bangaren darikar tijjaniyya watau farfesa sheikh ibrahim makari ya fara shan zazzaga daga malaman na izala wanda cikin wadanda suke fara zargin malamin har da daya daga cikin malaman da akayi mukabalar titsiye ga sheikh abduljabbar nasiru kabara.
Shi dai sheikh ibrahim makari ya tabbatar da cewa kalaman da sheikh abduljabbar yake amfani dasu wajen gudanar da karatukan sa sunyi nauyi amma sai dai hakan bazai hana ayi masa adalchi ba, sheikh ibrahim makari ya kuma tabbatar da cewa lika wa sheikh abduljabbar tuhumar zagin manzon Allah (s.a.w.w) rashin adalchi ne kuma hakan na iya sabbaba rikici gami da janye taimakon Allah cikin kokarin da akeyi na tabbatar da gaskiya.
Sai dai kalaman na sheikh makari basu zo ma malaman izala da dadi ba domin sun shiga ratattakar shehin malamin inda suke bayyana shi a matsayin mara ilimi kuma mai kokarin tabbatar da karya da kuma tada rikici
A bangaren mabiya darikar tijjaniyya ma dai an samu masu maida martani inda suke zargi malaman izala da cewa ba kare annabi ne a gaban su ba illah dai suna fakewa ne sunan kare annabi domin kare wasu mutane da suka daukaka su fiye da annabi (s.a.w.w)
Masu iya magana dai sunce dama dai garin kawai a farau farau din kawai yake karewa, Allah shi kyauta.
Ikon Allah