Wannan shi ne lokaci ma fi muhimmanci wanda ya dace ‘yan Nijeriya su sanya suyi nazari dangane da halin da Nijeriya take ciki, ta hanyar amfani da tabaran hangen nesan da zai haskaka turbar da ake tafiya a kai: shin akwai haske ko a cikin duffai ake, sannan a ayi nazari cewa daga wane zango aka taso, wanda ta hakan wala-allah a samu abin kamawa. Saboda a gaskiyar lamari halin da kasar da yan Nijeriya ke ciki bai yi kama da abinda hankali zai lamuta ya ci gaba da gudana ba.
A duk lokacin da ka ga hayaki ko shakka babu kowane lokaci gobara tana iya tashi, musamman a lokacin hubturu, mai kado sansamin gamji zuwa kasa kana ya lailaya su yi gaba tare da barin fako fayau.
A lokaci irin wannan akwai bukatar nazari na ta nutsu domin nemo mafita sahihiya wadda za ta dowo da al’amurra bisa kan turba mai karko, sabanin wanda ake ciki mai kama da rashin tabbas a rayuwa. Bugu da kari, yanzu ana iya cewa “Jiki Magayi”, yayin da kusan kowane dan kasa ke karbar kida a sama; ka waiga hagu da dama, gaba da baya, sama da kasa, shuru kake ji!
Malam duk da tafiya ce a tsakiyar sahara mai zazzafan yashi, babu alamar ruwa ballantana inwar bishiyar hutawa, amma dole ka samu yan mintunan da zasu baka damar tunanin me yake faruwa, saboda kai ma ka san tafiya a wannan yanayi ba zai yuwu ba- ok, kana tunanin gaba kura baya sayaki, a inda aka sanya a gaba? To bari ka ji, idan kana son ka sha labari tambayi falken da ya taba bin hanyar da ta ratsa rairayin hamada, alhalin guzuri ya kare, ka san abin da wuya gurguwa da auren nesa amma kuma mai rai baya rasa motsi.
Ga duk mai amfani da hankalin da Allah ya hore masa, idan ya yi tsam ya kalli yadda abubuwa ke gudana a rayuwar mu ta yau da kullum, musamman a yan shekarun nan, ya san da sake; wai an bai wa mai kaza fiffike. Kusan za a iya cewa komai ya canja daga muhallin da muka san shi, sannan kuma al’amarin rayuwa sai tsada yake karawa, abu yana nema ya zama ruwan zafi, tare da masaniyar kowanen mu kan cewa ana tafiya ba a kan turba mai kyau ba, kuma sannu a hankali mun koma tamkar rayuwar yan wuta, kullum kusan gara jiya da yau!
Har wala yau, abubuwa wasa-wasa sai kara tsukewa suke a wajen talakan Nijeriya, alhalin an gaya mana mulkin dimukuradiyya ya zarta na soja dadi nesa ba kusa ba, a baya mun ga yadda sojoji suka yi mulki har mun fara bukukuwan ban kwana da halin kangin da aka shiga, kwatsam sai muka lasa na farar hula, sai muka fara korafi da rakin cewa ya abin yake, har muka shiga na “Mai Malfa” muka ce shi ne mulki mafi muni tare da jefa Nijeriya cikin mawuyacin hali, ashe kunnuwa ne, jakkai na baya- Kaichon mu.
Haba Malam, da karfin cazbaha da lahaula muka kawar da mulkin da muke tsammanin daga shi an gama, muka botsare cikin fushi da tofin Ala-tsindire, muka ce fau-fau sai mun canja- na tsaya nan. Ai ko dan Lanjeriya ka ga canji, ciki har da na sulallah, kwabbai har da adajjo, daga cikin abinda dan Nijeriya ya zata shi ne daga ganin sarkin fawa, sai miya ta yi zaki. To yanzu dai anyi ruhin kan uwar dadi: kanta da lullubi amma bayanta a waje.
Ashe abinda muke kallo a matsayin matsi shi ne sauki, kana kuma abinda muke hangowa a matsayin mafita ashe lumbu-lumbu ne, wutar kaikayi ce. A rayuwar talaka mai karamin karfi, samun wadataccen abinci da kayan masarufi masu rahusa shi ne babban burin shi, idan an were harkokin tsaro wadanda sune kan gaba, muna sayen kwanon shinkafa naira 300 daga baya ya koma 1000 da yan kai, buhun masara 6000 yanzu ya koma sama da 18,000, sannan abu mai daga hankali shi ne hauhawar kayan abinci da masarufin sai ci gaba suke duk safiyar Allah.
A hannu guda kuma, shima tabarbarewar harkokin tsaron an iya cewa gara jiya da yau, wanda ko shakka babu haka abin yake ta nazari da yadda abin ke ta’azzara yana fadada kusan kowace rana, alhalin daya daga nauyin da ya hau kan kowace gwamnati a duniya shi ne samarwa yan kasa cikakken tsaro, a tsare rayuka da dukiyar yan kasa, idan an samu tazgaro a kan hakan, ya zama wajibi ga mahukunta su yi wa yan kasa cikakken bayani tare da neman afuwar su, chab wata miya sai a makobta. Ai na ga wasu kasashe idan an samu matsala a kowane bangare, haka mahukunta ke yi, su nemi afuwa kuma wani zubin su sauka daga mukamin su- sabanin Lanjeriyar dan Nijeriya.
Amma fa idan an bi ta barawo, to a bi ta mabi-sawu, tsaron kasa ko gina ci gaban kowace kasa hakki ne da ya rataya a bisa wuyan kowane dan kasa. Saboda haka matukar muna son ganin canji dole mu tashi haikan wajen bayar da tamu gudumawa da goyon baya a kowane janibi don kwalliya ta biya kudin sabulu. Me yasa wasu yan Nijeriya ba su da Nijeriya a zukatansu? Shin haka sauran kasashen duniya suke gudanar da harkokin kasarsu? Kuma shin ba ma tunanin cewa ba zai taba yuwa a ga daidai ba har sai mun daure mun aikata daidai da Kanmu?
Ko shakka bana yi wasu da daman yan Nijeriya suna tafiye-tafiye zuwa wasu manya da kananan kasashe a sassan duniyar nan, kuma ina kyautata zaton idon su a bude suna nazarin yanayin yadda kasashen ke gudanar da abubuwan ci gaban kasa ta hanyar nuna kishin kasarsu da al’ummarsu kusan fiye da kawunan su. Haka kuma suna sane da yadda suke sadaukar da koman su don ci gaban al’umma- suna matukar sha’awar kasashen sosai. Saboda idan ba haka ba, me yasa suke gogoriyon sayen manyan gidaje da zuba jaruka a kamfanoni a kasashen waje?
Kulli yaumin muna nazari na labaran yadda wasu yan Nijeriya suka mallaki kadarori a Dubai, Amurika, Landan, tare da kai yayan su karatu a manyan kasashen duniya tare da zuwa jniya a asibitocin wadannan kasashen- wannan ya nuna sun gamsu da su fiye da tasu kasar gado, alhali kudin kasar suke sace wa su gudanar da wadannan huldodin. Amma abin tambaya a nan shi ne: ta yaya wadannan kasashen suka habaka kuma suka bunkasa har suke sha’awarsu? Aljannu ne suka gina su ko al’ummar kasashen? Idan haka ne, me zai hana suma su zo suyi kokari irin na wadancan don gina mana Nijeriya? Ko dai akwai lauje cikin nadi?
Irin wannan sakacin da ya dade ana yi shi ya kaimu ga halin da muke ciki na rashin tabbas, mutanen nan marasa kishin kasa da al’ummarsu wadanda kullum babu kasar a zukatansu face kawai aljihunsu, sun yi dakon duffan zunubin da ya toshe ji da ganin su, wanda hakan ya jawo basa iya nazari na alhairi ko kadan daga gilashin zukatansu sun kai yan Nijeriya sun baro-Kaichon Nijeriyar Yan Nijeriya!