Har zuwa jiya talata 1 ga watan Nuwamba guguwar sabon zabe irin sa karo na biyar a kasa da shekara 4 ke kadawa a haramtacciyar kasar Isra’ila, a yayin da tsohon firayi ministan kasar Benjemin Natenyahu ke kokarin tabbatarwa ya dawo bisa kujerar shugabancin kasar.
Natenyahu dai ya sauka daga shugabanci ne ta karfi da yaji bayan wani hadakar jam’iyyun siyasa a kasar da suke yima lakabi da ”chanji” sun hada karfi da karfe waje guda suka kawo karshe tsohuwar gwamnatin sa bisa zargin sa da kasa kawo karshen Falasdinawa masu fafutikar neman ‘yancin su a hannun yahudawan sahayoniyan.
Amma sai dai sakamakon kasa kawo karshen lamarin da hadakar sukayi bayan sun dare karagar mulkin ya janyo rushewar hadakar tasu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasar mai ci, Yair Lapid ya nuna matukar sha’awar sa na cigaba da zama kan kujerar mulkin kasar amma kuma alamu na nuna bazai kai labari ba idan sakamakon zaben ya samu.
Alamomi na nuna yahudawan Isra’ilan sun fi karkatar da hankulan su kan dawowar Benjemin Natenyahu wanda a baya suka nuna basa tare dashi amma an samu canjin ra’ayi a wannan karon.
Dukkan alamomi dai na nuna Jam’iyyar Likud ta tsohon shugaban dai itace zatayi nasara a babban zab duba da yadda sakamakon zaben jin ra’ayoyin yahudawan ya nuna.
Natenyaho dai shine shugaba mafi sanuwa a tsakanin wadanda suka taba shugabantar Isra’ilan kuma ya shahara da kiyayya ga musulmi, musamman larabawa raunana ‘yan falasdinu.
An kuma shaide shi da kiyayya mai zafi dangane da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a tsawon shugabancin sa.
A wani labarin na daban kuma zanga zange ta barke a kasar Tunisiya sakamakon wata likita ‘yar asalin Tunisyan amma mazauniyar Saudiyya da hukumomin Saudiyyan suka yanke ma hukuncin daurin shekaru masu yawa saboda like da tayi a shafin tuwita.
Al’ummar Tunisiya dai sunyi kira da ayi gangamin kasa da kasa domin ceto rayuwar wannan Likita dake hannun mahukuntan Saudiyya.