Nafi gwamnatin jiyar Imo kudi dan haka banga abinda zan sata ba a cikinta_Sanata Rochas Okorocha
Sanata Richas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo wanda kuma a yanzu yake neman shugabancin Najeriya ya musanta zarge-zargen rashawa da satar kudi da ake masa lokacin da yake gwamna
Rochas ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a Channels inda yace shine ma yake bin gwamnatin jihar Imo bashi.
Yace da motocin sa ya rika amfani lokacin yana gwamna kuma bai karbi albashi ba, yace yana gidaje a Abuja sannan yana da makarantu da yake daukar nauyin karatun yara.
Ya kara da cewa akalla kullun sai ya kashe sama da Naira Miliyan 10 akan ciyar da wadannan yaran.
Yace duka nawane a gwamnatin jihar Imo da zai sata? Sanata Okorocha ya kara da cewa, bai ga abinda zai yi da kudin gwamnatin jihar ba.
Okorocha yace kai shi talauce wa ma ya kara yi bayan da ya zama gwamna a jihar Imo