Kamar yadda mayor na miami -dade, Daniella lavin cava ta bayyana adadin mutane da aka gano sun rasa rayukan su ya karu da mutum biyu idan aka kwatanta da rahoton karshe da aka wallafa inda yanzu adadin wadanda suka aka tabbatar sun rasa rayukan su ya kai ashirin da biyu sa’annan wadanda ba’a san inda suke ba adadin su dari da ashirin da shida.
Mayor Daniella ta tabbatar da cewa babban kokarin da mukeyi shine neman mutanen sa’annan da kokarin lalubo su raye.
Amma sai dai duk da wannan kokarin da su daniella sukeyi alamu suna nuna lallai a kwai sauran mutane masu matukar yawa a cikin ginin wanda ya jima da rugujewa.
Tace zamu cigaba da kokari sosai duk da wahalar aiki, tare da cewa dole ma’aikatan namu suka tsagaita aiki ranar alhamis sakamakon wani fiyif da suka tarar amma sun cigaba da aiki a yau asabar kuma muna sa ran cin nasarar cewo sauran wadanda suka rage a raye daga cikin ginin.
Manema labarai sun tabbatar da cewa a kalla sama da mutum dari ake sa ran suna cikn ginin wanda ya ruguje kuma suna fatan samun a ceto sauran rayuwar su wacce ta rage amma sai dai ga dukkan alamu aikin cewa wadanda ginin ya danne yana tafiyar wahainiya domin an dauki kwanaki kuma kamar yadda daniella mayor ta yankin ta bayyana tace idan sukayi iya bakin kokarin su zasu ruguje sauran abinda ya rage na katon ginin wanda a nasarin masana suna ganin rushe sauran ginin ka iya karasa sauran wadanda rayuwa ta rage musu a cikin baraguzan ginin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa amurka tana fama da matsaloli wadanda sike hada da annobar cutar korona, matsin tattalin arziki gami da dumamar yanayi gami a kan matsalolin rashin aikin yi da rashin matsuguni, sai kuma wannan matsala ta rushewar gininn a Florida.