Masu karatu assalamu alaikum. Barkan mu da warhaka, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan shiri mai muhimmancin da muke tattaunawa batutuwan da suka shafe mu mata da kuma iyalanmu.
A wannan makon na dauko wani batu mai muhimmancin gaske da yake taimakon iyali wajen dorewar zamantakewa da kyautata jin dadin rayuwa. Wannan batu kuwa ba komai ba ne illa tattali.
Tattali yana da muhimmancin gaske a rayuwa musamman wurin iyaye mata kasancewar suke sarrafa komai na cikin gida. Rashin yin tattali a wurare da yawa kan haifar da matsala a gidajen aure wani lokaci yana jawo rabuwar auren bakidaya. Yana da kyau uwa ta zama mai tattali har ta koyawa yaranta yin tattalin, daga nan za su tashi da dabiar kula da tattala abu.
Almubazzaranci ba abu ne mai kyau ba, musamman a yanzu da rayuwar ta zama abin da ta zama. Wata data ga yara sun tashi da dabiar Almubazzaranci amma sai su kyale su bazasu gyara musu ba, daga nan in sunje gidan aure suyi ta samun matsala.
Adana abu ne mai kyau da ya dace Kowani Dan Adam ya tashi da wannan dabiar, saboda a yanzu komai yayi tsada, abinda mutum zai saya guda biyar to yanzu bai wuce kudin biyu bane.
Ko namiji ke da dabi’ar rashin tattali yana da kyau a gyara masa balle mace,da za ta ja ragamar gida da al’umma. Rashin tattali muguwar dabi’a ce da take bukatar gyara tun daga matakin farko.
Don haka ‘yan uwana mata mu yi wa kanmu tattali, mu kiyaye almubazzaranci. Mu tabbatar da iyalanmu sun saba da yin tattali a rayuwarsu. Idan ba mu yi hakan ba, to fa akwai gagarumar matsala wacce za ta kai ki tashar da-na-sani, wanda kuma masu iya magana suka ce keya ce. Da fatan za mu yi aiki da darasin da batun wannan makon ya kunsa.
Allah ya sa mu dace, amin.