Rahotanni suna tabbatar da cewa manyan kasashen musulmi sun nuna halin ko in kula da lamarin babban malamin mazhabar shi’a dinnan watau malama ibrahim zakzaky, abin tambayar shine menene yasa hatta jamhuriyar musulunci ta Iran tayi shiru dangane da lamarin babban malamin.
Ya zama dole lamuran diflomasiyyar Iran kada su takaita Iran iayakokin kasar ta Iran, dole gwamnatin ta Iran ta tabbatar da taimakon ta ga magoya bayan ta kamar yadda kasar saudiyya takeyi, hakanan ma hatta kasar Isra’ila tana taimakon masu goyon bayan ta a duk fadin duniya amma menene yasa diflomasiyyar kasar Iran ba zata iya ceto rayuwar wannan babban malami ba?
Rahotanni sun tabbatar da cewa hujjatul islam wal muslimin wanda babban malami ne a kasar Iran ya koka sosai da gaske dangane da yadda gwamnatin Iran din ta kasa daukan wani babban mataki dangane lamarin malam zakzaky inda ya bayyana ba bukatar bayyana bambanci tsakanin musulmi balle kuma tsakanin dan adamtaka.
Hujjatul islam wal-muslimin fanahiyan ya tabbatar da cewa idan nhar Iran batayi kokari ta ceto mukawamar malam zakzaky ba hakan zai zama babbar matsala ga jamhuriyar musulunci ta Iran din.
Yanayin diflomasiyyar Iran dangane da zalunci da aka yima malam zakzaky baya da wani mataki daya dauka wanda hakan babban kuskure ne, Kamar yadda aka rawaito fanahiyan ya tabbatar.
Kasar Iran dai bata jima da aiwatar da zaben shugabancin kasar ba ind ake sa ran nan da wasu kwanaki sabuwar gwamnatin da ake sa ran zata kawo gyare gyare zata karbi iko.
Sabanin tsohuwar gwamnatin shugaba hassan rohani sabuwar gwamnatin shugaba Ibrahim ra’isi ana sa ran zatayi aiki na diflomasiyya sosai domin cewa wadanda ake zalunta a kasashe mabanbanta ciki har da jagoran mabiya mazhabar shi’anci na najeriya malam ibrahim zakzaky wanda babbar magoyin bayan jamhuriyar musulunci ta Iran ne kuma almajirin Aayatullah khumaini wanda shine jagoran jamhuriyar musuluncin ta Iran na farko.
Babbar tambayar da mutane ke tambaya shine, kamar yadda kasar saudiyya ta fito ta tabbatarwa da duniya cewa ta kaima malam zakzaky hari ne saboda yana goyon bayan Iran, to menene zai hana iran amfani da hanyar diflomasiyya domin ceto malam zakzaky daga hannun mahukuntan najeriya wadanda saudiyyan ke biya suna zaluntar malam zakzaky.