Mawaƙan Kano, Tagwayen Asali sun auri ƴan uwansu tagwaye
Fitattun mawaƙan zamani, Hausa Hip-hop a Jihar Kano, Tagwayen Asali, sun auri ƴan uwansu tagwaye, Hassana da Hussaina, ƴan asalin Jihar Katsina.
Tagwayen Asali sun daɗe su na jan hankalin magoya bayan su duba da irin shigar su iri ɗaya, su yi waka tare, sannan su na aiki a wata ma’aikata ta Gwamnatin Taraiya tare.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan biyun sun ce sun daɗe su na yin addu’a, har da ma azumi domin Allah Ya basu mata ƴan tagwaye da ga Katsina su aura.
“Mun dade muna addu’ar Allah Ya bamu mata ƴan biyu kuma sai gashi Allah Ya amsa addu’ar mu mun samu,” in ji su.
Ƴan tagwaye daban-daban ne su ka halarci ɗaurin aure da bikin na su domin su taya su murna da sa albarka.
Sannan kuma fitaccaen mawaƙin Hausa, Hamisu Breaker ne ya nishaɗantar da mahalarta a yayin bikin.