Biyo bayan kiran da gwamnan jihar katsina mal. bello masari yayi ga al’ummar jihar sa da cewa su fara koyon dabarun kare kai daga masu garkuwa da mutane wanda ciki har da amfani da dankon harbi domin kare kai, matasa masu kishin jihar katsina sun tattaru karkashin jagorancin bangaren ‘yan kafafan yada labarai na jam’iyyar PDP inda suka fara kokarin bama kai hoto a kan yadda zasuyi amfani da dankon.
Matasan wadanda suka fara lamarin kamar da wasa amma ya dauki hankalin kafafen yada labari kuma ya samu karbuwa daga al’ummar jihar kama daga matasa zuwa dattawa.
Masu gabatar da hoton sun tabbatar da cewa kamar yadda gwamnan jihar ya kirayi matasa su nemi dabarun kare kai kuma har ya ambaci amfani da danko wannan tasa suka ga dacewar shirya irin wadannan taro horaswa dom saukaka ma kai yadda ake amfani da dankon.
Wani matashi da muka tattauna dashi ya tabbatar mana da cewa, maimakon kowa yaje ya koyi nasa shi kadai idan aka hadu wani zai amfana daga wasu dabarun harba dankon wadda idan daban daban ne ba lallai ne wani ya amfana daga danarar da wani yake da ita ba.
Jihar katsina dai tana cikin jahohin arewacin najeriya wadanda suke fama da matsalar tsaro sakamakon kaka gidan da masu garkuwa da mutane sukayi a birni da kauyukan jihar wacce take kan iyakar najeriya ta nijar.
Alamu suna nuna gwamnati ta gaza gabatar da aikin daya rataya a wuyan ta mafi muhimmanci watau kare rayuwa da lafiyar mutanen ta, wannan ma tasa take kira ga mutane da cewa kowa ya kare kansa.
Danagane da ko wannan mataki da gwamnatin ta dauka na cewa kowa ya kare kansa yana da kyau ko akasin hakan wani dattijo da muka samu tattaunawa dashi cewa yayi, ba yadda za’ayi wanda ke rike da danko ya tunkari masu bindiga indai ba ya gaji rayuwa bane dama.