A Isra’ila tattare da cewa ba za’a iya tabbatar da cikakiyar samun nasarar Benjamin Natayaho a zaben shugabancin kasar ba har sai ranar alhamis amma tuni masu ra’ayin rikau na yahudanci gami da kyamar addinin Islama sun fara bayyana farin cikin su.
Hakan yana biyo bayan hasashen nasarar da Natanyahon ya samu a zaben wanda aka gudanar ranar talatar data gabata a fadin Kasar ta Isra’ila.
Benjemin Natanyaho dai wanda ya zame masa dole ya jira kammalallen sakamakon zaben wanda zai kai ranar alhamis kafin a bayyana kamar yadda jami’an gudanar da zaben suka bayyana amma hakan kamar ya kagarar da masu tsatstsauran ra’ayi mabiya dan takarar shugaban kasar.
Masu tsatstsauran ra’ayin na murna ne saboda nasarar Natanyaho wanda shima ana ganin mai tsatstsauran ra’ayi ne zata dawo da ra’ayoyin su bisa teburin gudanarwa gami da siyasar kasar ta Yahudawan Sahayoniya.
Amma sai dai masu fashin bakin siyasar cikin gida na Isra’ilan naganin dawowar ‘yan ra’ayin rikau bisa madafun iko zai haifar da rigingimun kabilanci gami da mazhaba a cikin gida da waje.
Hakan kuma zai iya lalata kyautata alakar da ake riyawa tsakanin Isra’ilan da kasashen larabawa irin su hadaddiyar daular larabawa, saudiyya da sauran su.
Masana sabgogin siyasa sun kuma bayyana cewa, dawowar Natenyaho da jam’iyyar sa mai tsatstsauran ra’ayi zata kara sanya raunanan Falasdinawa cikin halin ni ‘yasu, kuma itace zata kara rura wutar kwacen muhallan Falasdinawan.
Masanan sun kara da cewa hakan kuma shine zai sanya gwamnatin Isra’ilan taki barin Falasdinawa su kafa kasar su cikin sauki ba tare da fafatawa ba, hakan kuma zai haifar da gumurzu tsakanin Falasdinawa ‘yan asalin wajen da kuma bakin Yahudawan.
Ana kallon dawowar Natanyaho dai a matsayin karin matsala ga musulmi musamman Larabawa, Falasdinawa.
A bangare guda kuma ana ganin hakan karin aiki ne ga Jamhuriyar Musulunci ta Iranwa wacce fadi tashin ceto Falasdinawa daga zaluncin Yahudawan na Isra’ila.