Masu ruwa da tsaki a bangaren addinai na kasar Sin, sun yi watsi da rahoton baya bayan nan, wanda hukumar kare ikon bin addinai ta Amurka ko USCIRF ta fitar, inda a ciki ta soki kasar Sin da tauye hakkin bin addinai a cikin gida.
Rahoton wanda hukumar ke fitarwa duk shekara a bana ya soki manufofin kasar Sin na bin addinai.
To sai dai kuma masu ruwa da tsaki a bangaren daga kasar Sin, sun yi tir da shi, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin wata sanarwa da sakatariyar gamayyar kungiyoyin addinai ta kasar Sin ta fitar.
Rahoton ya bayyana yadda matsalar nuna wariyar launin fata yayi kamari a kasar amurka wanda ya kamata a lura da hakan amma abin mamaki amurkan ta buge da sanya idanu kana lamurran addinan wasu kasashen wanda hakan kamar yadda wasu masu lura da lamurran yau da kullum suka nuna bai shafi ita kasar amurkan ba.
A wani labarin na daban kuma fadar shugaban kasa ta yi bayanin cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya je asibiti ne domin duba ingancin lafiyarsa wanda ya saba yi duk shekara. Tuni Osinbajo ya koma Abuja inda ya cigaba da al’amuransa na yau da kullum kamar yadda ya saba.
Fadar tayi martani ga wani rahoto dake bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bashi da lafiya kuma an gan shi a asibitin Reddington dake Legas a ranar Asabar, 22 ga watan Mayu.
Kamar yadda wata kafar watsa labarai ta shafin intanet ta ruwaito, ganin Osinbajo a asibitin ya janyo tashin hankula da kuma tambayoyi daban-daban na dalilin zuwan mataimakin Shugaban Kasar asibiti.
Wasu daga cikin ‘yan najeriya sun shiga shakku gami da taraddudi dangane da ainihin halin lafiyar mataimakin shugaban kasar nasu inda suke ganin kamar ana boye musu yanayin halin lafiyar sa ne, kamar dai yadda ake zargin gwamnatin maici da boye yanayin halin lafiyar shugaba janaral buhari.