Biyo bayan dambarwar da ta kaure tsakanin wasu daga cikin malamai a jihar kano da kuma babban malamin nan sheikh Abduljabbar nasir kabara inda wasu daga cikin malaman suke tuhumar malam abduljabbar din sda cewa ya danganta wasu kalamai wadanda suka taba shaksiyya mai tsarki ta manzon rahama (s.a.w.w) hakan ta tilasta ma babban malamin addinin musulunci dinnan mabiyin darikar tijjaniya watau sheikh ibrahim makari ya gabatar da wani jawabi wanda ya kawo mafita daga cikin dambarwar da ake ciki.
Sheikh makari ya bayyana cewa da farko bai so ya sanya baki a wannan dambarwa da take faruwa ba amma saboda yadda lamuran suka lalace ana nema a canja alkiblar lamurran ya ga dacewar tofa albarkacin bakin sa.
Da farko dai malam makari ya bayyana rashin dacewar jiyar da al’ummar annabi
(s.a.w.w) irin wadancan munanan hadisai saboda haka baya da bukatar saurarar ire iren wadancan hadisai domin ta tabbata karya ake yima manxzon rahama saboda haka gujewa saurarar su shine yafi alfanu.
A karshe malamin yayi kira ga malaman maja da suji tsoron Allah domin ba’a yakar bata da bata, inda ya bayyana yunkurin malaman maja din na danganta zagin manzon Allah ga malam Abduljabbar da cewa rashin adalchi ne kuma hakan na iya sawa a gamu da fushin Allah ta’ala.
Babban malamin na tijjaniyya wanda kuma shine babban limamin kasar najeriya yayi kira ga gwamnatin jihar kano dama malaman maja da su guji azarbabi ko kuma amfani da wannan lamari domin daukan fansa a kan malam abduljabbar.
Zuwa yanzu sheikh abduljabbar yana hannun jami’an tsaro yayin da ake sa ran ranar 28 ga watan yuli za’a cigaba da shari’ar da gamayyar malaman maja suke kalubalantar sa.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa an bukaci almajiran malam Abduljabbar da su kwantar da hankali domin gaskiya zatayi halin da da yardar Allah ta’ala.