Makircin Amurka da kawayenta
Shugaban Amurka Biden ya bada sanarwar cewa, nan da bada dadewa ba zesa a gina tashar jiragen ruwa a Gaza domin a gaggauta kai agaji a zirin.
A jiya ne kuma Isra’ila tace: a yau za ta dauki matakin kame kudancin gabar din tekun Gaza.
Idan kuka hada labaran biyu.
Hakikanin labarin shine, Biden yana so da wannan dalilin a hukunce ya shigo da sojojinsa cikin zirin Gaza.
Wanda hakan ze temaka wajen dakile hare-haren da Hamas take kaiwa Isra’ila.
sojojin ruwa na kawayen Amurka ma za su tafi kai tsaye zuwa wannan mahallin da Amurka din zata gida.
Kafa sansanin Amurka a zirin Gaza ba komai ba ne illa wata dabara ta goyawa Isra’ila baya kai tsaye a wannan mawuyacin halin, don rage matsin lambar da kungiyar Hamas ke yi wa sojojin Isra’ila a wannan yanki.
Inda zaku gane girman karairayi da sharrin mahukumtan yamma shine: mashigar kan iyaka a Rafah, Masar ta kasance lafiya amma a rufe, kuma dubban daruruwan ton na kayayyakin abinci ne ke rubewa a wajen anki bari a shigar dashi cikin zirin Gaza din.
- duba nan: 👉👉 Dambe Warrios Tayi Aniyar Zamanantar Da Wasan Dambe
A maimakon bude wannan hanyar, Amurka da kawayenta suna yin wani yunkuri ne na ban dariya😂 sannan suna kokarin kwantar da hankalin al’ummarsu dakuma rage matsin da akai musu a kafafen yada labarai.
Bugu da kari: burin da ake da shi shi ne rufe gabar tekun Palasdinu da kuma mayar da tashar iskar gas ta Mari gaba daya zuwa Isra’ila, wanda kuma wani bangare ne na wannan shiri na dogon lokaci.