Kamar yadda tsohon sanatan kaduna ta tsakiya ya wallafa a shafin sa na tuwita, ya bayyana kin amincewa da kudurin na janye haramcin tuwita da majalisar ta wakilan najeriya tayi a matsayin babban abin takaici, inda ya nuna tsananin bacin ransa gami da alhini.
Tsohon sanatan ya cigaba da bayyaana cewa hakan kamar tauye ma ‘yan najeriya ‘yancin su na fadar albarkacin baki ne kuma hakan bazai haifarwa da najeriya da mai ido ba.
Wasu daga cikin masu bibiyar tsohon sanatan a shafij nasa nan tuwita sun tofa albarkacin bakin su inda wasu da dama suka goyi bayan ra’ayin tsohon sanatan kuma suka bukaci gwamnatin najeriya dama majalisar wakilai da ta dattijai su gaggauta yin mai yiwuwa domin dauke wannan doka a kan kamfanin na tuwita mai yawan masu amfani dashi a fadin kasar ta najeriya.
Idan ba’a mance ba dai a watan daya gabata ne gwamnatin najeriya karkashin jagorancin shugaba muhammadu buhari ta haramta amfani da manhajar ta tuwita kuma ta shelanta hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama yana amfani da manhajar ta kamfanin tuwita a fadin kasar.
Gwamnatin ta najeriya ta dauki wannan mataki ne sakamakon goge wata wallafa da shafin shugaban kasa muhammadu buhari yayin a kan ‘yan kungiyar biyafara masu rasjin ballewa daga tarayyar najeriya inda kamfanin na tuwita ya bayyanan cewa wallafar ta shugaban kasa bata bisa ka’ida amma sai dai gwamnatin najeriyar bata dauki lamarinn da sauki ba domin tana ganin hakaan kamar cin fuska ne ga gwamnatin da kuma shugaban kasa muhammadu buhari.
‘Yan najeriya da dama musamman masu amfani da manhajar da tuwita basu ji dadin wannan hukunci da gwamnatin ta najeriya ta dauka amma babu yadda suka iya domin dokar ta shafi kowa da kowa dake najeriya.
Amma sai dai wasu daga cikin ‘yan najeriyar sun samo wata hanya ta amfani da manhajar VPN domin canja muhalli wanda hakan kan basu damar bijirewa dokar gwamnatin gami da yin amfani da manhajar ta tuwita.
House of Representatives rejection of the lifting of the ban on Twitter is unfortunate and condemnable.This is a disappointing and disgraceful example of legislative support for the executive suffocation of the freedom of expression.They are historically in sync with autocracy.
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) July 2, 2021