Kungiyar ta (OPCW) wacce take ikirarin tabbatar da cewa an haramta amfani da makami mai guba a fadin duniya, ta kuma tafka wata gundumemiyar karya domin kare kagen da tayi ma gwamnatin siriya a shekarun da suka gabata inda tayi dalilin shigar amurka da kawayen ta kasar da sunan yaki da amfani da makami mai guba a cikin kasar ta siriya.
A ranar 14 ga afrilu na shekarar 2018 kasar amurka, faransa da ingila suka kai harin hadin gwuiwa a garin douma wanda yake da nisan kilomita goma daga birnin damascous babban birnin kasar ta siriya.
Amurka da kawayen ta sun zargi gwamnatin siriya da karya dokar kasa da kasa ta shekarar 2013 wacce ta sama hannu dangane da amfani da makami mai guda.
An tabbatar da cewa wadanda sukayi binciken makamin mai guba a douma a shekarar ta 2018 basu samu wani alami na amfani da makami mai guba ba amma sai suka tabbatar cikin rahoton su cewa sun samu alamun anyi amfani da makami mai guba domin su bama amurka, faransa da birtaniya damar shiga kasar ta siriya.
Bayan samun matsin lamba daga kasar amurka da sauran kasashen turai kungiyar mai ikirarin haramta amfani da makami mai guba tayi wata dabara inda ta nuna cewa ta sake tace binciken nata na shekarar 2018 duka a kokarin ta na rufa karyar da ta tafka a rahoton nata tun farkon lamari.
Dama dai gwamnatin rasha da ta siriya a wurare mabambanta sun sha bayyana cewa masu binciken waccan kungiyar sun samar da rahoton karya ne dai domin su bama amurka da kawayen ta damar shiga kasar ta siriya da kuma aiwatar da abinda suke so wanda zuwa yanzu basu fita daga kasar ta siriya ba.
Kamar yadda kafar sadarwa da Press T.v ta tabbatar tun lokacin da amurka da kawayen nata suka shuga kasar ta siriya zuwa yanzu ba’a samu zaman lafiya a kasar ba.