Mai magana da yawun bangaren nujaba wanda wani bangare ne na kungiyar ‘yan asalin iraki masu sa kai domin tabbatar da tsaro a fadin kasar ta iraki yayi Allah wadarai da ayyukan ta’addanci kan ‘yan kasar da iraki da amurka take aiwatarwa ba dare da rana kuma ya bukaci gwamnatin ta iraki da ta dauki mataki kan wadannan ayyuka da sojoji baki ‘yan kasashen ketare karkashin jagorancin amurka da kawayen ta suke aiwatarwa.
Nasr-Aalshammari wanda shine mai magana da yawun kungiyar ya bayyana cewa amurka itace kasar ta tafi kowacce kasa karya dokokin kasa da kasa a duniya kuma ya tabbatar da cewa a kwai bukatar gwamnatin kasar sa ta iraki tayi kokarin korar amurka daga kasar ta iraki domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar ‘yan kasar ta iraki.
”Amurka ta karya duk dokokin kasa da kasa kuma ta tabbatar da cewa canjin gwamnati bazai canja yanayin ayyukan ta na ta’addanci a iraki dama yankin gabas ta tsakiya ba” Inji Al-shammari.
Kwanakin da suka gabata ne dai amurkan ta kai harin kan mai uwa da wabi a kan iyakar iraki da siriya inda ta kashe da dama wasu kuma suna raunata, cikin wadanda suka rasa ransu har da wani da jariri.
Tuni dai gwamnatin iraki tayi Allah wadarai da wannan aikin ta’addanci na amurka kuma ta bayyana cewa zata dauki dukkan matakan da suka dace da dokokin kasa da kasa domin nuna ma amurka kuskuren ta domin amfanin irakawa da kuma zaman lafiyar su.
Amurka dai tana da sansanonin sojoji da yawa a cikin iraki dama fadin gabas ta tsakiya wanda akayi ittifakin zaman sojojin amurka a yankin na gabas ta tsakiya shine babban dalilin da ya sa aka rasa zaman lafiya a yanki.
Wani masanin lamuran yau da kullum daga jamhuriyar musulunci ta Iran ya tabbatar da cewa dole sai an kori amurka daga nahiyar sannan za’a samu zaman lafiya.