Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da shugaban dandalin yada labarai na Harka Islamiyya Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai, ta ce hukuncin da kotu ta yanke ya yima dukkan magoya bayan Harka Islamiyyaa Najeriya dadi.
Ranar jiya Laraba ne Babbar kotu a jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi a kansu wanda akansa ne a aka tsare su tsawon shekaru kusan shida.
Wannan hukunci na kotu dai ya wanke Sheikh Ibrahim Zakzaky da maidakinsa daga dukkanin tuhumce-tuhumcen da ake yi musu, wanda gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar ga kotun, kuma an salli shari’ar ne saboda babu wasu hujjoji da suke tabbatar da abin da ake zarginsu.
Yanke wannan hukunci da babbar kotu a kaduna tayi shine ya kawo karshen zaman jagoran mazhabar shi’a na afirka a hannaun gwamnati na tsawon kusan shekara shidda.
Masu lura da lamurran yau da kullum dai suna kallon wannan nasara a matsayin babbar alama da take nuna cewa malamin da mabiyan sa sune ke da gaskiya a bisa tataburzar da ta faru a disambar 2015, wanda tun wancan lokaci ake tsare da shehin malamin.
Gwamnati dai ta sanar da cewa ta kaima shehin malamin da almajiran sa hari ne saboda tare hanya da aka yima tsohon babban hafsan sojin ksa General Yusuf Tukur Buratai, amma daga baya ta tabbata ba wannan ne dalilin kai ma malamin da almajiran sa hari ba.
Babban abinda yake tabbatar dakan shine hukuncin da kotu ta yanzke din wanda yake karyata duk waccan farfagandar da aka dingi yadawa tsawon shekara shidda.
Majiya mai tushe tana tabbatar da cewa ga dukkan alamu harin ya biyo bayan bukatar kasar saudiyya na tabbatar dav cewa da murkushe akidun da suka saba da nata, wadanda suka hada da darikun sufaye da shi’anci inda aka fara zakaran gwajin dafi a kan shi’anci a shekarar ta 2015.;