Kamar yadda kafar sadarwa ta Mehr ta rawaito, shugaban jami’an tsaro na kerman ya tabbatar da cewa, tarukan tunawa da shahadar kasim sulaimani na cigaba da gudana a birnin Kerman dama sauran garuruwan Iran bakidaya, kuma mutanen gari ne ke gudanar da tarukan.
Sardar Muahmmad nazari ya tabbatar da cewa, a wajen taron manema labarai wanda ya gudana a safiyar lahadi ya tabbaar dacewa, Sulaimani alamin maktabin imamai da kuma shahidai ne kuma yana da halaye na musamman tattare da shi.
Ya cigaba da cewa, mafi muhimmanci daga halayen Sulaimani kamar yadda jagoran juyin juya halin musulunci shine gaskiya da kuma cika alkawari sa.
Nazari ya cigaba da isahara da cewa, muna cikin lokacin tunawa da shahadar Sulaimani karo na shida, ya kuma jaddada cewa, satin gwagwarmaya zai kuma daga ranar 12 zuwa 18 ga watan dei na Iraniyawa a birinin Kerman wanda za’a gudanar da tarka masu tasiri musamman ga manyan gobe.
Nazari sa’annan ya kuma jaddada lura da siffofin Kasim sulaimani na dakiya da kuma cikawa Allah alkawari, yace Sulaimani baya neman a san shi kuma wannan alama ce ta tabbatar da cewa yana yi ne domin Allah.
Ya cigaba da cewa, jagoran juyin juya hali ma yayi ishara da wannan kuma ba mamaki hakan ne ma yasa hanyar hajj kasim sulaimani ta zama maktaba, kamar yadda jagoran ya kira ta da makaranta kuma maktaba.