A wata fira da akayi da babban lauya barista Ishaq Adam a gidan talabijin na Al-wilaya T.v , babban lauyan ya bayyana cewa tabbas kama shahararren malamin nan sheikh Abduljabbar da akayi gami da maka shi kotu da malaman maja na kano ta hannun gwamnatin kano suka yi cewa hakan ya sabawa dukkan tanadin dokokin da kundin tsarin mulkin najeriya ta tabbatar.
Tun da farko babban lauyan ya fara bada amsar tambayar da akayi masa ne dangane da almajiran malam zakzaky da aka kama kuma ake zargin su da gudanar da gangamin lumana a babban birnin tarayyar Abuja.
Barrister Ishaq Adam ya bayyana cewa a n cigaba da sauraron shari’ar ‘yan uwa sittin inda a cigaba da sauraron shari’ar , sakamakon gabatar da bukatar korar karar da lauyoyin almajiran malam zakzaky syukayi kuma lauyoyin gwamnati suka lura kotu zata tabbatar da hakan sukayi hanzarin kara caje cajen da suke yima almajiran malam zakzaky din wanda hakan ya karawa shari’ar zango domin dole sai an kuma saurarar sabbin tuhume tuhumen bangaren lauyoyin gwamnatin.
A bangare guda kuma lauyan ya tabbatar da cewa an fara gudanar da sauraren karar da diyar malam kabiru masaka daya daga cikin wadanda aka kama kuma ya rasa rayuwar sa a hannun ‘yan sanda, wanda hakan ya sa diyar sa fatima kabiru masaka ta shigar da kara domin neman hakkin jinin mahaifin ta.
Daya juyo bangaren bada amsa dangane da kama babban malamin sheikh dakta Abduljabbar, barista Ishaq Adam ya tabbatar da cewa a matsayin sa na daya daga cikin lauyoyin malamin sun tabbatar da cewa an zalunci wanda suke karewa domin an kaishi kotu ba a lokacin aiki ba kuma an hana shi ‘yancin samun lauyan da zai kare shi.
A karshe barrister Ishaq ya tabbatar da cewa wannan aikin masarautar saudiyya ne kuma ya ja hankalin ‘yan siyasar kasar mu da subi a hankali domin bama wata kasa damar shiga cikin sha’anin ‘yan kasa cin amanar kasa ne kuma ba karamin laifi bane.