Hukumomin jamhuriyar Nijar sukace suna gudanar da bincike dangene da wani kazamin hari da aka kai gidan Seini Oumarou, kakakin majalisar dokokin kasar da manyan bindigo, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daya daga cikin dagororinsa yayin da wani na biyu kuma ya samu mummunan rauni.
Da yake shaidawa manema labarai, mai baiwa kakakin majalisar shawara Osseni Salatou, yace harin wanda aka kaishi a daren Juma’a wayewar Asabar, wasu mutane biyu kan Babura ne suka kai shi.
Ya kara da cewa sai da suka kafa bindigar mai sarrafa kansa a gaban gidan kafin su harbe dogarin shugaban majalisar har lahira, kafin su raunata na biyun sa.
Ma’aikatar cikin gidan Nijar ta tabbatar da kai harin a cikin wata sanarwa da yammacin Asabar, inda ta kara da cewa maharan biyu sun yi kokarin tuka wata motar 4×4 da ke tsaye a gaban gidan ba tare da samun nasara ba kafin su arce.
Seini Oumarou, mai shekaru 70, shi yazo na uku uku a zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Disambar 2020, kafin ya marawa Mohamed Bazoum baya kuma yayi nasara.
Matsalar tsaro ta mamaye kasar Nijar dama makotan kasashe irin su najeriya libiya saboda kaka gida da kasashen ketare sukayi a al’amuran tsaron kasashen.
Ana fatan a samu canji mai kyau a lamarun tsaron kasashen yammacin afrika amma hakan bazai taba samuwa ba dole sai an karkade hannayen kasashen ketare musamman na yammacin turai daga lamuran tsaron wadannan kasashe na afirka.
Tasirin kasashe irin su saudiyya, Isra’ila Amurka da, Faransa da Ingila da sauran su.