Yayin da muka cika shekaru uku da shahadar Janaral kasim sulaimani kuma aka gudanar da taruka gami da jawabai a sassa daban daban na duniya dangane da wannan rana ta shahadar Kasim Sulaimani, munci karo da wani jawabin Malam Zzakzaky dangane da wanna rana.
Jawabin wanda Ofishin Malam Zakzkay suka saki a shafin su na Tuwita kuma Malamin ya sanyawa hannu ya bayyana Kasim Sulaimani a mastayin babban gwarzo kuma abin koyi wajen fada da ta’adanci.
A jawabin Malam Zakzaky yace, muna cika shekaru uku da rasa babban mujahidi kuma abin koyi a bangare gwagwarmayar fada da ta’addanci wanda kuma kisan sa yadda tona asirin asalin ‘yan ta’adda.
Zakzaky ya cigaba, Amurka ta bugi kirjin daukar nauyin wannan hari na kisan Kasim Sulaimani kuma hakan yake tabbatar da cewa sune kanwa uwar gami a ta’addancin gabas ta tsakiya musamman a Iraqi da Siriya, inda suke da kala kalan ‘yan ta’adda da sunaye mabambanta irin su DAESH da ISIS.
Jagoran gwagwarmayar ya cigaba da cewa, tabbas sun aikata babban kuskure da suka kashe Kasim Sulaimani domin na farko sun tonawa kan su asiri, na biyu kuma sun wanzar da ambaton sa, sun wanzar da ambaton sa da wannan kisa kuma sun wanzar da hanyar gwagwarmaya da ya bada rayuwar sa gareta.
A karshe Malam Zakzaky yayi addu’ar Allah yayi rahama da Kasim Sulaimani da Abokin sa Abu Mahdi Almuhandis da sauran wadanda sukayi shahada tare wajen neman ‘yanci a gabsa ta tsakiya dama sauran duniya baki daya.
Sheikh Zakzaky ya kuma yi fatan abinda su Kasim Sulaimani suka kafa zai wanzu cikin nasara har zuwa nasara ta karshe (InshaAllah) a kan zaluncin duniya tare da kafa tsarin adalchi a gabadayan duniya.
Idan ba’a mance ba Sheikh Zakzaky dai ya samu fitowadaga kurkuku ne bayan babbar kotu a Kaduna ta wanke shi daga laifukan da gwamnatin kaduna ta zarge shi da su.